HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 7️⃣

HUKUNCE HUKUNCEN HAILA GA MAI AZUMI 7️⃣



🔷 Tambaya:- Idan mai haila ko mai jego tayi tsarki kafin alfijir ya keto amma batayi wanka ba sai bayan fitowar alfijir shin azuminta ya inganta??

🔶 Amsa:- Eh azuminta ya inganta, domin awannan lokacin sun kasance cikin wanda azumi ya wajaba akansu, hukuncin ta irin hukuncin mai janaban da baiyi wanka ba sai bayan fitowar alfijir, saboda faɗin Allah {amma yanzu babu laifi ku rungume su, ku nemi abunda Allah ya farlanta muku, sannan kuci kusha har farin zare ya bayyana muku daga baƙin zare na daga alfijir}
   Idan har Allah ya yarda da ayi jima'i har zuwa fitowar alfijir kenan wanka dole ya zama bayan fitowar alfijir, haka kuma yazo acikin hadisin Nana Aisha Allah ya Kara mata yarda tana cewa "Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance yana wayan gari (alfijir ya na fito masa) alhali yana mai janaba, alhali yana azumi"
Ai hadisin yana nufin Manzon Allah baya wankan janaban sai bayan fitowar alfijir".

📝 المصدر :
[ ٦٠ سؤالا في أحكام الحيض والنفاس/لفضيلة الشيخ محمد بن صالح العثيمين رحمه الله ص١٢].

# Zaurenfisabilillah 

https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)