HUKUNCIN ƊAUKAR HOTO

HUKUNCIN ƊAUKAR HOTO


*TAMBAYA*❓
:
SHIN DAUKAN HOTO DA MUKEYI DA Handsets.KO Cameras. HALAL NE / KO HARAM ?
:
*AMSA*👇
:
Malamai sunyi saɓani akan hukuncin hoto, inda wadansu malamai irinsu (Nasirudden Albani) sukeda fahimtar haramcin hoto kai tsaye indai ba na laruraba, kamar Fasfo (passport) na aikin hajji ko na shiga wata qasa dai kokuma dai duk wani hoto wanda larurace take hukunta ayishi toh sukace wannan babu laifi saboda larura, amma hakanan kawai dan gayu ko wani abu ayi hoto sukace bai halasta ba
..
Amma irinsu ( Usaimin) idan kaduba fatawarsa zakaga yayi wani tafsili me ban qaye wanda muma akanshi muke, wato muna tareda fahimtarsu ( usaimin)
.
Malamin yace:
haramunne ayi zanen duk wata halittar Allah, kamar zana hoton mutum ko akuya ko kaza ko jaki kawai mutum yazauna yana zana hotonsu wannan kaitsaye haramunne, wannan ya kunshi har hotunan da akesa yara yan primary suna zanawa na dabbobi, dakuma wanda yake sana,ar zana hoton mutane, kawai mutum yazauna ana kallonshi ana zana surarshi ahoto wannan dukansu haramunne.
..
Amma hoto na camera sukace wannan babu laifi, baya cikin kwaikwayon halittar Allah matukar baza,ayi editing ba, shi wannan editing din haramunne.
Masamman sanya fuska a wani gangan jiki da abinda yai kama da hakan.
wannan haramunne kwarai da gaske
..
Amma dai shima
hoton cameran sukace kar ayawaita a ɗan yinshi sama sama, musamman ga namiji sukace idan kabiyema yawan daukar hoto sekuma kazama tamkar ɗan daudu.
.
_Aduba fatawa ta (Ibn usaimin) za'aga tafsilinda yayi insha Allahu, hakama acikin littafin usulut tafsir yadanyi tsokaci gameda hakan.

Wallahu A'alam

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)