JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 01

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 01


MA'ANAR ADDINI
Masu nazari kan addinai suna fassara ma'anar addini ne da cewa: Wani tsari ne na rayuwar al'umma dake tattare da ilimin da ya shafi lamuranta kacokan, da wasu hada-hada na gamayya da za a riqa yi a wasu lokuta na masamman, gami da dabi'u da nazari ko imani da wasu abubuwa da ake ganin gaibi ne, sai littafai saukakku ko qagaggu ko wurare masu tsarki dake buqatar ziyara, sai kuma annabci, akwai kuma qungiyoyi wadanda galibinsu sun kafu ne don isar da mutum ga abinda aka tsarkake ko ake ganin ya saba wa fahimtar dan adam, ko kuma girmansa ya kai yadda za a sallama masa, akwai wasu abubuwan kuma da suke buqatar imani kawai ba tare da wani binciken qwaqwab ba, a qarshe dai suka nuna cewa cikakken ma'anar addini abu ne mai matuqar wahala kuma babu ma wanda ya iya kawo shi a kammale (Morreall, John; Sonn, Tamara (2013). "Myth 1: All Societies Have Religions". 50 Great Myths of Religion).
.
Abubuwan da ake gani wadanda ke fito da ma'anar addini fili a nazarinsu sun hada da tarurruka na gudanar da wani abu na bauta, sai hutsubobi, bukukuwan addini, wani nau'i na ban girma da ake yi wa wani abu ko mutum mai rai ko matacce, ba-da-rai ko lokaci ko kudi kan wani abu na bauta, yanka, bukukuwan dake da alaqa da bauta, al'amuran da suka shafi mutuwa zuwa birne gawar, aure da zamansa da abubuwan dake kan ma'auratan, salloli da yadda ake yinsu, kida-kide da aka alaqanta su da bauta, raye-raye tare da kida ko babu, al'adar mutum da wayewarsa (Faith and Reason by James Swindal, in the Internet Encyclopedia of Philosophy an ajiye shi a 17/4/2017).
.
Sai kuma abubuwan da aka rubuta a littafai da ake ganin suna da tasiri da rayuwar al'umma, kamar tarihin addinin da gwagwarmaya, hukunce-hukunci, da fassarar abubuwan da suka faru ko wadanda aka yi imanin za su faru. A muslunce kuwa malam Alawiy bn Abdilqadir As-Saqqaf (Mai kula da farfajiyar Ad-Durar As-Sunniya wace aka tanaje ta kan manhajin Sunna wal Jama'a) yana fadin cewa: Addini dai shi ne qudurta tsarkin bin bauta tare da aikata duk abinda zai nuna qanqar da kai gare shi gami da miqa wuya cikin qauna da kwadayin rahamarsa da tsoron uqubarsa. Wannan fassarar ta hada addinin da Allah ya turo annabawansa da shi ko kuma wadanda mutanen suka qirqirar wa kansu suke ta haqilo a ciki.
.
MENE NE MUSLUNCI?
Tambayar da aka yi wa mariganyi Bn Bazz kenan, shugaban kwamitin da'awa da fatawa a lokacinsa, an buga shi a shafinsa na yanar gizo inda ya ba da amsa da cewa: "Muslunci shi ne miqa wuya ga Allah da sunkuyo gare shi don gudanar da wani aiki ko wani umurni tare da nisantar ababan haninsa, Allah SW yana cewa {Tabbataccen addini a wurin Allah shi ne muslunci} Al-Imram 19. Muslunci na nufin miqa wuya da qanqan da kai ga Allah wurin kadaita shi da tsarkake bauta gare shi, sai kwatanta abinda ya yi umurni da nisantar abinda ya hana wannan shi ne muslunci.
.
Ya ce: "Daga cikin abinda ya sanya wa bayi akwai: Salla, ba da zakka, azumin Ramadan, aikin haji, bin uwaye, sada zumunta, nisantar sabo gaba daya duk yana cikin muslunci, an kira addinin da muslunci ne don qanqar da kai da ake yi ga Allah da shirin amsar duk umurnin da ya yi, kwatanta umurninsa cikin tsantseni da sallamawa don kwadayin falalarsa". Wannan da kake gani shi ne babban dalilin jayayya da sabanin da muka sami kammu a ciki yau, koda yake tun tale-tale haka abin yake ba wani canji aka samu ba, daga mai kore addinin ya ce babu, ba wani Allah sai mai qoqarin cewa shi ne Allan kai tsaye a bauta masa, sai mai 'yan dabarbaru.
.
Wani kuma ya yarda da musluncin kuma yana kiran kansa musulmi amma fa so yake ka yarda Allah ya amince da shi, har ma ya ba shi matsayin da ya bambanta da na sauran mutane, ko su ce Allan ya ara masa wasu ayyukansa wanda bai baiwa kowa ba, a qarshe ya buqaci a riqa masa wata hidima ta masamman, saboda yana da wani sirri ko ilimi na boye da Allah ya ba shi wanda ba kowa yake da shi ba, wasu kuma matsalarsu da sahabban Annabi SAW ne, sai matansa, da 'yan uwansa da ma saqon da Annabi SAW din ya bari, suka ce an canja komai hatta Qur'ani, shi ya sa komai nasu daban ne, daga tauhidin, salla, azumi da sauran shika-shikan.
.
Wasu kuma gani suke kowa fa a kan kuskure yake, in kuma bai gyara ba to hukuncinsa kisa, sun kafurta wanda za su kafurta, suka ce suna kira ne zuwa ga zallar muslunci amma fa musulman suke yaqa, suka maida jinin musulmi kamar na kaza ga kafurancan ba su damu da su ba. Akwai masu tafiya daidai da hukuma ba tare da sun duba umurni da hani ba, suka bi manyan malaman al'umma suka soke, sai ka taras da qaramin yaro wanda bai yi nisa a karatu ba yana aibanta sunan babban malami, ya bata karantarwarsa gaba daya su ma wadannan sunanan.
.
Akwai wadanda ke aiki da sunan addini wurin neman jagoranci, gashi dai musuluncin suka ambata amma ba su damu da wace aqida kake dauke da ita ba, in dai za ka yarda da manufar tafiya tare wurin isa ga shugabanci shikenan ka zama dan uwa, a taqaice dai duk wadanda muka ambata kowa na iqirarin shi ne a kan hanya madaidaiciya, har da wadanda suke ganin Allah na da diya da wadanda suke cewa su kadai Allah ya zaba kuma ba zai qona su ba. Tafiyar na da nisa Allah ya yi mana jagora.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)