*MUGUN ABOKI...................*
👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬
*FUTOWA TA 👇*
*(1)*
*WANE NE ABOKI*
*ABOKI* shi ne mutumin da bashi da ko wacce irin alaqa ta jini da wani mutumin na da ban, sai dai alaqa ta unguwa ko makaranta ko wajan aiki ko wani wajen na daban ya maye waccer alaqar ta jini, zai zamewa mutum kamar dan uwa na jini.
*ABOKI* shi ne mutumin da ake dogara da shi a lokacin da mutum ya shiga cikin Qunci, shi ne mutumin da baka iya boye masa sirrikanka, kuma baya jin kunyar ya nuna rauninsa agabanka, kuma yana sauri wajan ya yi maka afwa ya yin da ka zame a wani abu ko kuma kayi wani kuskure duk girmansa ko qanqantarsa, shi ne mutumin da kake jin da di da nutsuwa ya yin da kake tare dashi, shi ne mutumin da yake kare mutuncika da kuskurenka ya yin da baka nan, shi aboki mutum ne da alaqa ta kimantawa da girmamawa da darajta wa ce mai qarfi tsakaninku, kuma ba'a gina wannan abokantakar ba domin neman wani amfani na dan Adamtaka ba.
*RABE-RABEN ABOKAI*
Abokai sun rabu gida uku :
*1- Aboki mai neman amfani*
*2- Aboki mai neman jin dadi*
*3- Aboki mai neman falala*
*1- Aboki mai neman amfani* shine wanda zai yi abota da kai mutuqar yana anfanuwa da kai ta wajan kudi ko alfarma ko wani abun na daban, idan wannan abun ya yanke daga gareka, zai zama maqiyinka bai sanka baka san shi ba.
Irin wannan abokin mai neman amfani ya zama ruwan dare a wannan zamanin misali abokinka ko kawarki ta kusa yana daga cikin mafi daraja awajanka shima haka, amma wataran ya tambayeka aran littafi sai kace masa nima ina da buqatar karanta wannan littafin gobe, sai ya yi fushi da kai ya dawo yana adawa da kai shin wannan aboki ne? Amsar shi ne a a aduk lokacin da kaga mutum baya abota da kai sai dai idan zai amfanu da wani abu to kasani cewa maqiyinkane ba aboki bane.
*2- Aboki mai neman jin dadi* shi wannan nau'in na aboki ba zai taba abota da kai ba sai dai idan ya zauna da kai zai samu nishadi wajan fira ko debe kewa ko firar dare, sai dai shi ba ya amfanuwa da kai kaima baka amfanuwa dashi babu abun da yake gudana tsakaninku face bata lokaci. Aduk lokacin da kaga mutum bazai yi abota da kai ba sai dai idan zai shagaltar da kai da janka guraren hutawa to kasani wannan babu wani Alkhairi tare dashi. Yi qoqari shima wannan ka nisan ceshi saboda kada ya bata maka lokutanka.
*3- Aboki mai neman falala* shi wannan nau'in na abokin zai dauke ka zuwa ga duk wani abu wanda zai kawata ka, ya nisantar da kai daga duk abun da zai munanaka, zai bude maka duk wata qofa ta Alkhairi, kuma zai nusantar da kai akanta, idan ka zame a wani abu zai yi sauri wajan fuskantar da kai fuskar da baza'a zar geka ba akan wannan zamiyar da kai, wannan irin abokin shine abokin da ake san ka dage wajan neman sa kuma idan ka same shi shi yi qoqari wajan riqesa da fiqoqinka domin ragowar babu Alkhairi atare dasu .
*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*
*MU HADU A FUTOWA TA 02*
*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
*Dalibai masu neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
*(Abu Rumaisa)*
🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
*(UMMU HANAN)*