KASHE TSAKA ABUNE MAI KYAU

KASHE TSAKA ABUNE MAI KYAU
:


*TAMBAYA*❓
:
Aslm.allah y gafarta mlm y kuma karawa mlm lpy dan allah mlm menene tarihin tsaka dakuma dalilin dayasa ake kasheta?

:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Tsaka dabba ce mai nau'in ƙadangare amma ba takai kadangare girma ba, kuma tafi rayuwa acikin dakuna.

addinin musulunci Addini ne mai tsafta da son zama lafiya, don haka ne ya shar'anta mana wasu ababe da suka halatta mutum ya kashe su daga ciki ma akwai wanda idan ka kashe kana samun lada, daga cikin wadannan halittu akwai tsaka! Wacce Annabi saw ya kira ta da cewa lallaifa ita tsaka algun-guma ce  wacce kuma Annabi saw ya tabbatar mana da cewa lallaifa dukkan wanda ya kashe tsaka a duka guda daya rak! To yana da lada dari (100)

Daga cikin laddubar kashe tsaka itace anaso a lokacin da kaga tsaka sai kayi kwadayin kasheta to kayi basmala wato kace Bismillahi sai ka kai mata duka idan Allah ya kaddara ajalinta yayi shi kenan sai ka ambaci Allah ka kasheta, ko meye dalilin yin Bismillah a lokacin da mutum namiji ko mace yayi nufin kashe tsaka? Dalili kuwa shine saboda Al'janu suna zama tsaka, kuma sukan zama kunamu (scorpions) sukan zama macizai (snake's) saboda haka ne Annabi yace mutum ya ambaci Allah a lokacin da mutum ya nufaci kashe tsaka!

Mutane da yawa basu damu da su kau da tsaka a gidajen su ba saboda basu dauke ta wata abar da zata ta tada hankalin masu gida ba.

GA WASU DAGA CIKIN ILLOLINTA MASU BAN TSORO

1 – Idan aka bar gari a bude takan shiga tayi birgima a cikin garin , bayan an tuka wannan garinakan kamu da cutar baras wato kuturta ko wasu mugayen kuraje

2 – Idan aka bar ruwan sha a bude sai tayi amai a cikin ruwan, yawanci sai kaga an kamu da shanyewar jiki ko kuma lalacewar sassan jiki.

3 – Idan mutum ya kwanta barci bai yi addu’a ba takanyi busa a cikin idon mutum sai kaga ya wanci an samu lalacewar gani mai kyau ko a makance.

Kwanan baya an samu labarin wata mata da ta dafa shayi da tsaka a cikin butar shayina sandiyyar wannan tsaka da mijinta da yayanta duk suka bakunci lahira.

4 – Idan tsaka ta rika a gida tana iya haddasa gobara, misalin ire-iren gobara da take faruwa a yanzu. Sau da dama tsaka ce amma bamu sani ba domin ita tsak tana tare da mugayen Aljanu.

Mu kula da wannan dabba tsaka wanda take mu’amala a cikin gidajen mu, mu kula da abincin mu da abin shan mu domin mu kaurace ma wannan illa na wannan dabba. Da zaran an ganta a cikin gida ayi kokarin kasheta kuma a ambaci sunan Allah domin tana tare da shaidanu, tana iya cutar da mutane. Ayi amfani da tsintsiya ko takalmi wajen kasheta ko kuma a saka mata maganin kashe kwari.

Domin korar tsaka a gida,ka nemi gishiri ka gauraya da garin tafarnuwa ko danyar tafarnuwa sai ka watsa a duk inda kake yawan ganin ta a gidan ka,tsaka zata bar wajen a cikin gaggawa.

Allah ya kare mu sharrin ta.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)