JININ HAIHUWA YA QI TSAYAWA HAR BAYAN KWANA 40, SAI MIJINA YA SADU DA NI, YA HUKUNCINA?
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum. Don Allah Malam mene ne hukuncin matar da take jinin haihuwa Mijinta ya sadu da ita? Duk da tayi 40 amma har yanzu tana ganin alaman shi, ta fada mishi bai tsaya ba! Amma ya ki yarda duk da dai ba zuba yake yi ba, wasu lokuta har tana fara sallah, wani lokaci idan tana tsarki ta wanko wajen sai ta ga alamun yauki da kalan jini, mene ne hukuncinta?
:
*AMSA*👇
:
Wa'alaikumus salam, malamai sun bayyana cewa; shi jinin haihuwa ba shi da qarancin kwanaki, matuqar ya ɗauke wa mai haihuwa ko da kafin ya cika kwana 40 ne, to za ta yi wankan tsarki ta ci gaba da yin ibada, sannan kuma mijinta zai iya saduwa da ita. In ma ya qara dawo mata ne, to sai ta dakata da ibada, da zarar ya cika kwana arba'in (40) ko da bai dakata da zuwa ba, to shi kenan sai ta yi wankan tsarki ta ci gaba da yin ibada, kuma mijinta zai iya saduwa da ita. Kwana arba'in shi ne iya tsawon kwanakin jinin haihuwa (nifasi), da zarar ya cika kwana 40 bai ɗauke ba, to shi kenan ya zama gurɓataccen jini, babu laifi idan mijinta ya zo mata tana wannan jini, tun da ta cika kwanaki arba'in. Wato dai cikin kwanaki arba'in ɗin nan ne ba a yarda miji ya zo wa matarsa ba.
Allah ne mafi sani.
*Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.*✍
Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇
https://wa.me/+2348087788208
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ