KUNYA (1)
🔶 MENENE KUNYA??
Kunya wani chanji ne da rauni da yake bijirowa mutum na daga tsoron aikata abinda za'a aibanta shi akai.
Ibnu Allan Allah ya masa rahama yake cewa "kunya wata ɗabi'ace da take gadar da barin aikata mummunan abu na magana ko aiki, kuma ɗabi'ace da take hana mutum tauye haƙƙin wani mai haƙƙi".
دليل الفالحين ٣/١٥٨
Fadlullahi Al-jailani Allah ya masa rahama yake cewa "kunya wani chanji ne da yake bijirowa mutum alokacin da yaji tsoron azargeshi akan wani abu da yake mummuna ne".
فضل الله الصمد ٢/٥٤
🔷 KUNYA NA DAGA CIKIN SIFFOFIN ALLAH
Yana daga cikin siffofin Allah subhanahu wata'ala kunya, kamar yadda yazo acikin hadisi ingantacce Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake cewa "Lalle Ubangijin ku mai kunya ne kuma mai karamci, yana jin kunyan bawansa ya daga hannu ya roƙeshi har ya sauƙe bai amsa ba".
Fairuzabadi Allah ya masa rahama yake cewa aƙarƙashin wannan hadisin "Amma kunyan Allah subhanahu wata'ala wani nau'i ne da hankula basa iya riskarsa kuma bazasu iya kwatanta tashi ba, kunyane na karamci da kyauta, domin shi Ubangiji yana kunyan bawansa ya ɗaga hannu ya roƙeshi har ya sauƙe hannun bai amsa masa ba, sannan yana kunyan ya azabtar da furfuran da ta samu mutum a musulunci".
بصائر ذوي التمييز ٢/٥١٧
🔶 RABE-RABEN KUNYA
Al-Munawi Allah ya masa rahama yake cewa "kunya ta rabu kashi biyu;
1. Kunya ta ɗabi'a wacce Allah ya dasata acikin zuƙatan mutane gabaɗayansu, misalinta shine; buɗe al'aura agaban mutane, duk wani mutum mai cikakken hankali yana kunyan ya bude al'auransa agaban mutane, haka saduwa da mace afili.
2. Kunya ta imani wanda shine mutum musulmi ya kame daga aikata abinda Allah ya haramta saboda tsoron sa".
التوقيف على مهمات التعاريف ١٥٠
Duka nau'ka guda biyu na kunyan nan an haɗawa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama su, a kunya ta ɗabi'a Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yafi budurwar da take cikin haudajinta kunya, a kunya kuma na imani Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya kasance shine mafi ƙololuwa awannan ɓangaren.
Mu haɗu a rubutu na biyu in Sha Allah
Julaibeeb
30/12/2021
# zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah