KA NUTSU KA GODE MA ALLÃH!!! (Rubutu Na Daya) 0️⃣0️⃣1️⃣

KA NUTSU KA GODE MA ALLÃH!!! (Rubutu Na Daya) 0️⃣0️⃣1️⃣ 


A kullum Rayuwa kafi Wani ne Wani ya fika ba a taba Zama Daya arzikin kowa Kuma a hanun ALLÃH yake.

Kwantar da hankalin ka Ka tuna ni'imomin da ALLÃH YA maka Ka kirga wadanda ALLÃH Bai Musu ba Kar ka Dinga kirga wadanda suke sama da kai. 

Ka Yi Kokari Ka bi shawarar baban Alqasim Mai Gidan mu Annabi Muhammad SallalLÀHU Alayhi Wa Àlihi Wa Sallama Wacce ya bayar a hadisin da imamul Bukhariy ya rawaito Daga Abu Hurairah RadhiyalLÀHU Anhu Cewa:
"انظروا إلى من أسفل منكم ولا تنظروا إلى من هو فوقكم فهو أجدر ألا تزدروا نعمة الله عليكم"

Ku Dinga duba wadanda ke kasa da ku Kada ku Dinga duba wadanda ke sama da ku Wannan Shine mafi kusa Wajen katange ku daga butulce Wa ni'imar da ALLÃH YA Muku. 

Da wannan Zamu Fahimci Cewa Rayuwa Akwai wadanda suka fika akwai kuma wadanda kafi su in ko haka ne toh kullum Ka Dinga duba Na kasa da Kai. 

Kada Ka saka damuwar Wani a zuciyar Ka don ya fika wata Ni'ima har ta Kai ga Zuwa ga hassada. Hassada fada ce da rabon ALLÃH Don Duk Wanda Ka gan Shi Cikin Ni'ima ALLÃH Ne Ya Masa in Kana Jin haushin Sa toh lallai kana fada ne da rabon ALLÃH in ko Haka ne toh ALLÃH YA na tambayar ka Ka bada amsa
أهم يقسمون رحمة ربك نحن قسمنا بينهم معيشتهم فى الحياة الدنيا ورفعنا بعضهم فوق بعض درجات ليتخذ بعضهم بعضا سخريا 
Shin su suke Rana rahmar Ubangijin Ka? (Ba su bane) Mu ne Muka raba Musu Rayuwar su a tsakanin su sannan muka Daga darajar Wasun su Akan ta Wasu sabida su Rike su a Matsayin isgili. 

ALLÃH YA Kare mu daga Cutar hassada. 

Mu Hadu a Rubutu Na biyu

Dan uwan ku a Musulunci
 *AbdulMannan Mahmoud Shira (Abu Ruqayyah)* 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)