YADDA ZA KA TATTALA GIRMANKA.
1. Ka daina kallon wanda ba ya kallon ka.
2. Ka daina roko.
3. Ka daina yawan surutu, fiye da buƙata.
4. Idan Mutane suka wulaƙanta ka, ka kawar da kan ka daga gare su.
5. Ka rage yawan yadda kake ziyartar mutane, musamman waÉ—anda ba su ganin darajar ka.
6. Kar ka ci Abincin Mutane, fiye da yadda suke cin na ka.
7. Ka damu da kan ka, ka sanya kan ka farinciki.
8. Ka daina annashuwa akan gulmar wasu.
9. Ka yi tunani kafin ka yi furuci. Kaso tamanin cikin É—ari (80%) na dalilin da yasa mutane suke girmama ka, daga Bakin ka ne.
10. Kodayaushe kayi iya kokarin ka. Ka sanya tsabtatattun tufafi.
11. Ka zama mai cim ma nasara. Ka tashi tsaye akan muradun ka.
12. Ka girmama lokaci.
13. Kar ka ci gaba da kasancewa a alaƙar da ba a girmama ka, kuma ba a ganin darajar ka. Ka fice, ka yi tafiyar ka.
14. Ka koyi yadda za ka kashewa kan ka kuÉ—i. Ta hakan ne mutane za su koyi yadda za su kashe kuÉ—i a kan ka.
15. Haka kawai wasu lokutan a neme ka a rasa.
16. Ka zama mai bayarwa, fiye da yadda kake karɓa.
17. Kar ka je inda ba a gayyace ka ba. Kuma idan an gayyace ka, kar ka tsaya fiye da Maraba.
18. Ka É—abi'anci mutane, kamar yadda ya dace da su.
19. Sai dai in wanda yake bin ka Bashi, missed call biyu ya wadatar, idan suna daraja ka, za su kira ka.
20. Ka yi gaskiya a cikin ayyukan da kake yi.
Fatan Alheri.
© Prof. Sufyan