MACEN DA BA A IYA SAKI 18

*MACEN DA BA'A IYA SAKI............* 

🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕🧕

         *FUTOWA TA 👇*
                  *(18)*
  
KADA KI SIFFAN TAWA MIJINKI WATA MATA

   Ya "yar uwa mai daraja ina gargadarki da siffan ta wa mai gidanki "yar uwarki, kawarki, makociyarki, ko wacce irin mace ce domin shaidan zai iya saqa masa kaunar wannan matar acikin zuciyarsa wanda akarshe lamarin bazai miki da diba, ko dai ya yi kokari wajan aurota kina gani, idan kika tada masa da hankali kuma zai iya rabuwa dake kuma ya auro ta idan ya samu damar haka. 
   Shi yasa manzan rahma yake cewa "kada mace tayi tsirara gaban "yar uwarta mace, sai ta siffan tawa mijinta surarta kamar yana ganinta". 
 Wani mutum yake cewa matarsa kada ki siffan ta min wata mata a gaban idona.
   Don haka "yar uwa mai daraja ki zama mace mai kishin mijinta ta hanyar nisantar siffan ta masa ko wace irin mace ko da tana da wannan abun, muddun kina nisantar aikata haka kece macen da nakewa laqabi da macen da ba'a iya saka.
  
*FATAN ALKHAIRI GA MA'AURATA*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

*MU HADU A FUTOWA TA 19*

*Rubutawa... ✍️✍️✍️*
*Dalibi mai neman ilimi*
*Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏


Post a Comment (0)