FALALAR KIYAYEWA GA NAFILFILI JERARRU

FALALAR KIYAYEWA GA NAFILFILI JERARRU


Daga Ummu Habiba matar Annabi (SAW) tace; Na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su k'ara tabbata gare shi yana cewa: "Babu wani Bawa musulmi da Zai yi Sallah ga Allah a kowace rana raka'a goma sha biyu (12) na nafila bana farillah ba face se Allah ya gina masa wani gida a Aljannah, ko kuma se an gina masa wani gida a cikin Aljannah, Ummu Habiba tace ban gushe ba ina Sallatan su bayan wannan.
.
{Muslim, cikin littafin Dariqus-Salihin}
.
Note:
Wad'annan nafilfili jerarru (Rawaatib)sune, hudu kafin Azzuhar, biyu bayan Azzuhar, biyu bayan Magrib, biyu bayan Isha'i, biyu kuma sune raka'a biyu da ake yi kafin Asuba.
.
Mu Sani ba wanda zai cika farillai, ya kuma dage da nafilfili face se ya samu soyayya gurin Allah.
-Allah ya bamu ikon kiyaye su tare da kyakkyawan niya da Ikhlasi (Amin)

# Zaurenfisabilillah 

Telegram:
 https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Zaurenfisabilillah-107455768160058/?ti=as
Post a Comment (0)