WANE TANADI KA YI MA KANKA GAME DA SADAKA MAI GUDANA?

WANE TANADI KA YI MA KANKA GAME DA SADAKA MAI GUDANA?? 



💧Sahabi Abi Huraira ya ruwaito hadisi daga Manzon (SAW) yana cewa: "Lallai yana daga cikin abinda yake riskar mumini na aikin sa da ladarshi bayan mutuwar shi;
● Wani ilmi da ya koyar da shi, kuma ya yaÉ—a shi.
● Da ÆŠa nagari da ya bari. 
● Da kuma wani Alqur'ani da ya gadar da shi. 
● Ko kuma wani masallaci daya gina. 
● Ko wani gida ga matafiya da ya gina shi. 
● Ko wata Æ™orama da janyo. 
● Ko wata Sadaqa da ya fitar da ita daga cikin dukiyarsa, a lokacin lafiyar shi, a halin rayuwar shi.
To, wannan duka zasu riske shi a bayan rayuwar shi.

 Ibn Majah, kuma Al-baniy ya ingantashi. Duba (Dariqus salihin)

Note:
 • Sadaqa mai gudana (Sadaqatu Jariya) shine duk wani aiki da ladan sa bazai yanke maka ba har bayan ka mutu.

• Malamai suka ce fadin Manzon Allah (SAW) "ko wani É—a na gari" . Ai idan ka dace da É—a nagari da yake aikata alkhairi zaka rika samun lada.

• "Ko wani AlÆ™ur'ani da ya gadar" ma'ana, ya rubuta wani mus'hafi na Alqur'ani ya barshi ake karantawa, ko ya saya ya bayar, ko mutum ya bar nashi aka dauka ake karantawa. Zai rika samun lada.

Allah Ta'ala ka azurtamu da ayyukan alkhairi da zamu riƙa samun ladan su bayan rayuwar mu.

# Zaurenfisabilillah

Telegram:
 https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)