FITAR MATA ZUWA SALLAR IDI 002


FITAR MATA ZUWA SALLAR IDI 🕌🚶🏿‍♀

002

Malaman mazhabar shafi'iyya sun kayyade fitar mata sallar idi da cewa ban da masu kyakkyawar Kama. Imam Nawawi ya ce a cikin Al-Majmu' (5/13):

Shafi'i da malaman mazhabarmu, Allah Ya ji kansu, sun ce: Mustahabbi ne ga mata ba masu kyakkyawar kama ba, su halarci sallar idi. Masu kyakkyawar kama kuwa makaruhi ne su halarce ta. Har inda yake cewa:

Idan matan suka fita sallar idi, to Mustahabbi ne gare su su fita ba da tufafin ado ba, kada su sa tufafin da za su sa su fita daban. Kuma Mustahabbi ne gare su su tsaftace jikinsu da ruwa, amma ba a so musu su shafa turare ba. Wannan duk hukuncin tsofaffin mata ne, waďanda ba a shā'awarsu, da makamantansu. Amma yarinya, da kyakkyawar mace, da wadda ake sha'awar kamarta, su waďannan makaruhi ne su halarci sallar idi, saboda tsoron fitina a gare su, ko sabo da su. To, idan aka ce wannan ai ya sa6a wa hadisin Ummu Adiyya wanda muka ambata, sai mu ce: ya zo a cikin sahihain daga Aisha (R.A) ta ce: “Da manzon Allah (ﷺ) ya riski abin da mata suka tsiri yi, da ya hana su kamar yadda aka hana matan Bani Isra'ila.” Sannan kuma fitinu da hanyoyin sharri a waďannan lokutan sun yi yawa, sa6anin lokacin farko, Allah dai Shi ne mafi sani.”
.
Na mu zamanin kuwa ya ma fi tsanani. 

Imam Ibnul Jauzi ya ce a cikin littafin Ahkamun Nisa'i (shafi na 38):

Mun yi bayanin cewa fitar mata halal ce, amma idan ana jin tsoron fitina gare su, ko saboda su, to hana fitar ta fi falala. Domin matan zamanin farko sun kasance a kan tarbiyya ta daban da matan nan, haka ma mazan.... 

Wato sun kasance a kan tsantseni sosai. 

Daga waďannan ruwayoyi da zantuka na malamai, ya 'yar uwa musulma, za ki san cewa an ba ki dama a cikin Shari'a ki fita domin sallar idi, amma da sharaďin lizimtar ďa'a, da kame kai, da kunya, da kuma nufin neman kusanci ga Allah, da haďuwa da musulmi a cikin bikinsu, da bayyana alamomin addinin musulunci. Ba wai manufar ita ce a bayyana kwalliya, ko jefa kai cikin fitina ba. Don haka ki faďaka da wannan. 

Allah Ya sa mu dace. 

✍🏿Ayyub Musa Giwa.
(Abul Husnain).
09/08/2019.

*Daga Zauren*
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*
Post a Comment (0)