MAI YATSUN BAIWA ﷺ

MAI YATSUN BAIWA ﷺ
*************************


Bukhari da Muslim sun ruwaito ta hanyar Sayyiduna Jabir 'dan Abdullahi (Allah ya yarda dashi) yace :

"Mutane sunji kishirwa sosai aranar Hudaibiyyah alhali Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yana zaune da wata kwarya agabansa yana alwala da ruwan cikinta sai mutane suka taho wajensa aguje. 

Sai ya tambayesu "MAI YA SAMEKU NE?".

Sai suka ce "Bamu da ruwan da zamuyi alwala dashi ko wanda zamu sha, sai wannan dake gabanka".

Da ya sanya hannunsa acikin kwaryar, sai ga ruwan nan yana kwararowa ta tsakanin yatsunsa tamkar idaniyar ruwa. Sai muka sha kuma mukayi alwala".

Wanda ya karbo hadisin daga Jabir yace "Shin ku nawa ne awajen?".

Sai yace "Koda mun kai dubu dari da ruwan nan ya ishemu. Amma dai mu dubu goma sha biyar ne".

Ya Allah yi salati ga Annabin da ka fidda ruwa ta tsakanin yatsunsa masu albarka, adadin dukkan Qasa da ruwan dake duniya. Tare da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa baki daya. Ameen. 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (14-08-1440 20/04/2019).
Post a Comment (0)