HALIN YAU 23 & 24

🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•


         *SADAUKARWA GA*
        *SADIK ABUBAKAR*.



    *Fatan alheri ga marubuciya*
     *Zainab Ilyas Mazawaje*.





                    23_24.





Tsananin matsin da Uncle Mukhtar ya mata yasa ta zama shiru shiru, ta matu'kar rage kaudi da iyayyi.

Kullum tana ri'ke da littafan koyon turanci, ire-iren su Teach ur self.

Ta sake mannewa Safina Bunkure. kasancewar Safeena girman Lagos ce, mafi yawan maganarta turanci ne, dan haka ba ta yarda su yi magana da hausa tare da safina, itama kuma Safina ba ta gajiya da gyara mata a inda ta ji ta yi kuskure.

Ba'a dauki lokaci mai tsayi ba,ta fara rage tsoron kar ta yi turanci a mata dariya, ganin ta na iya mayar da magana cikin harshen da ke mata nauyi, sai kuma ta mai da hankali akan ragowan darussan gaba 'daya.

Ta matu'kar rage shiririta, yanga, da hirar soyayya, da duk wata sharholiyar da su ke, abu 'daya ne ba ta bari ba, kwalliya, wadda wannan kam a jinin ta ne.

Su Halima cewa su ke basu ga Malamin da zai uzzura mu su, babu dalili basu yi maganin sa ba.

Ita ko tsaki take ja a fili, ta yi shiru.
A zuciyarta ko cewa take ai ku ya ga kun iya turanci, kuma yana ganin yadda ake zuwa 'daukan ku a motoci na garari,
ni kuwa ya ga ba ko 'daya, ba dole kowacce shara ya debo ya juye a kaina ba.
Tabbas tana takaicin yadda ita kadai ya ke gallazawa.

Shikuma ganin yadda ta yi laushi ta kuma maida hankali kan karatun ta, sai ya sassauta mata, duk kuwa da zai yi wahalar gaske ya yi darasi bai ce ta tashi tayi bayanin yadda ta fahimci darasin ba, kawai dai kyara da disgin ya rage.

A haka har suka yi jarrabawar mock wadda duk 'dalibi ya ke tsoro da fargaban kar ya fa'di.

Ana yin hutu da kwana biyu mijin Sumayya ya turo takanas a dauki kannen shi 'yan mata guda biyu da yar autar dakin su, da kuma wadda suka hada uba yar amaryar Baban su, sai ya ro'ki Baffah! akan ya basu Sa'adah ta yi musu hutu tare da 'kannen shi. ba musu ya amince, har gida suka zo suka dauke ta, sannan suka dauki hanyar jos kwata, ta yamma da Bauchi😀.
 
Wannan hutun yana cikin abubuwan da Sa'a bata Mantawa da shi, domin kuwa ta yi matu'kar jin dadin zama da 'kannen Idris yadda suka kasance yara kamammu, marasa hayaniya amma kuma yan kwalliya ne na sosai, shiyasa abotar su ta yi da'di.

 Sumayya kuwa ba ta matsa musu, hatta abinci wadda suke so shi zata ce su yi, mai gidan kuma kusan kullum sai yasa direbansu ya zaga dasu, sunga gari, da wuraren sha'katawa , sannan kuma duk fita sai ya basu kudin kashewa, wadda ba abin da suke siya sai kayan kwalliya ko dai abin da ya shafi sutura.

Ba abin da ya dame su illah tunanin mock exam din da suke fargaban fitowar ta, tunda dukkan su set daya suke Amma makaranta daban daban.

Haka suka 'kare hutunsu cikin jin Dadi da mutunta juna, da kanshi Idris ya kawo su har gida tare da kayan tsarabar ni'ki ni'ki, barin ma dankalin turawa da dangin su cabbage da Kara's, harta atile kamar wadda za'a ci a tsawon wata.

Baffa da Inna sai godiya suke,tare da sake godiya ga Allah, na yadda Sumayya ta sami mijin daya San alheri yake kuma rama alherin da kyautatawa da mutunci.

Barinma idan ta zauna tana bawa Inna labarin daular da Anti Sumayya ke ciki, sai dai ta yi murmushi mai nuna yadda zuciyar ta ke cikin farin ciki.

Ba zata yi magana ba sai dai ta bige da cewa kema Allah ya ba ki mijin rufin asiri, yasa ki dace kamar na yar'uwarki.

Ita kuwa kai tsaye take cewa
 "Amma fa Inna gaskiya ni bana son irin tsarinsa, ace mutum duk inda matarka zata fita kace sai ta zumbula hijabi har 'kasa, kuma wai dole sai ansa safa? ko 'dan wanne mazahaba ne?"

Cikin mamaki Innar ta zuba mata ido, tare da tafa hannu tana sallallami tace
"ke kuwa Iyah wannan tsarin da yake yi na martaba shari'a ne bai Miki ba?

Na mijin kwarai shi ke kishin matarsa, ya 'dora ta akan ka'idojin shari'a, wadda zasu gudu tare su kuma tsira tare!
"Daular da ya sanyata a ciki ta burge ki, kina kuma fatan ki samu irinta, amma abin mamaki, hijabin da Ubangiji ne yace a saka shine bai miki ba?
Anya Iyah, Baffan ku bai yi kuskuren barinki shiga wannan makarantar da ta ke sake girmama burinki ba?"

Da sauri tace
"Haba mana Inna! ni fa ba cewa nayi kar asa hijabi ba, gani na yi tana da tsala tsala dogayen riguna tunda ga kan yan 'kasashen Oman, Qatar, Saudi, Dubai, masu tsadar gaske masu kauri, amma wai dan 'kauyanci kuma sai akawo hijabi a maka, bayan su karan kansu hijaban ne".

Ta fa'da tana fashe wa da dariya.

Allah ya shirye ki kawai, Inna ta fada tare da mi'kewa ta yi tsakar gida, tana fadin wannan dogon burin na ki yana ban mamaki Iyah.
Ban da 'karya da fariya, da kai kanka inda Allah bai kai ka ba, gidan uban wa kika san 'kasashen da suke sarrafa riguna masu tsada?
 
Naga dai ke kam baki da halin samun su, ban da Allah ya miki gata ya baki yar'uwa mai halin girma tana baki kuncen su, wasu ma ko saka su bata yi, ta ke baki, amma har ki zauna ki karkace baki kina min lissafin inda ake sarrafa su?".

Ta cika fam saura 'kiris ta fashe cikin turo baki tace
"Amma Inna abin har da gori?"

Da sauri tace

"Eh dole na goranta miki, dan na ga nema kike ki manta cewa ke'din ba yar kowa bace, face malam Basiru mai 'yar tireda😀wadda ko hanyar inda jirgi ya ke sauka ba ki ta'ba zuwa ba,
Amma kina bada labarin 'kasashen duniya, wallahi Iyah ki canja wadannan halayen da nake ganin kina sake arowa kina yafawa".

Shiru Sa'a tayi amma takaici ke cin ta shikenan sai mutum ba zai fadi ra'ayin sa ba?
Sai a hau mishi gore-gore, har a nemi cewa ya raina shari'a?

 Hawaye ya siraron mata, ta goge ta tashi ta yi 'dakinta, tana fatan Allah ya bata miji mai kula da iyali kamar Idris, amma ba mai a'kidunsa na asalin bahaushen arewa ba.

Kayanta na makaranta ta shiga fitowa dasu tunda ga kan uniform, sandal, school bag dukkan su sabbi ne, ta shiga shirya su ta yadda gobe sai dai ta dauka a kammale.

Ba tasan meyasa ta ke 'dokin komawa makarantar ba wannan karon? domin kuwa tunda Mk Bichi yaje makarantar ko hutun weekend ne fargaban zuwan Monday take yi.
Wata'kila kuma dan ta sami sau'kin kunyata ta da yake yi ne.

Amma Kuma duk da sau'kin da ta Sami a bangaren shi, haushin shi da tsanar shi na nan cike a zuciyar ta.
 kwanukan abincin su ta wanke su tas kafin ta kammala wanke wanken har gawayin ya fara kamawa, dan haka ta cika tukunya ta dora ruwan wanka, tana gama wanke kwanukan, sai kuma ta hau share tsakar gidan hadi da wanke dan matsakaicin bandankinsu, kafin wannan lokaci kuma ruwanta yayi zafi, ta juye ta shiga wanka! bayan ta maida ruwan kunu da ta jefa mishi tsamiya kan wutar.

Tana fitowa a wanka innarta ma ta fito tsakar gida, tana ganin yadda Sa'a ta gyare mata gida tsab.

Da'di ya kamata na yadda ko kadan Iyah bata da son jiki.
Ba zato ta ji anrungumeta tare da cewa 

"morning Innah" 
Ture ta tayi tare da cewa 

"oh ni kam Ina kallo a gun ki".
 
Dariya tayi tare da fadin "Inna gaisuwar kawai shine abin kallon"?
  
Wuceta ta yi tana bude ruwan dake Kan gawayi, ganin yana shirin tafasa yasa ta fara shirin dama kunun, ita kuma sa'a tayi 'daki tana shiryawa.

Cikin 'kankanin lokaci da dama kunun, ta kuma dauko fulawar data kwaba a 'karshen dare dan yin fanke, ganin ta tashi sosai yasa ta maida mai kan wutar tana shirin suya, tana kwashe kaskon farko Sa'adatu na fitowa ta shirya amma bata sanya uniform ba.

Ganin yadda innarta ke kwaso fanke yayi brown ya tashi sosai, da'di ya kama Sa'adatu.

Sai kawai tafara rawa tana juyi tana wa'kar

"Mamana, mamana! mai sona, mai tattalin zuciyata".

Kwafa Inna ta yi tana fadin "zanga sadda za ki girma Iya"

"Idan Kinga na girma sai kin haifa min 'kani ko 'kanwa".

Ta wuce ta dauko, kofi da plate tana fadin "Allah Inna Ina son 'kanne gashi Anti Sumayya tayi min nisa bare na dinga debo su Khalifa".
Ta fa'da cikin muryar tausayi tamkar hakan zaisa innar ta haihu yanzu yanzu.
 
Numfasawa Inna ta yi sannan tace
"Ai kin kusa samun 'ya'ya ma indai kina da rabo, ba'di iyanzu ai kina dakin ki ".
Daure fuska tayi, sannan tace
"Nifa sai na fara karatu".

Da sauri Inna tace "Inma karatun za ki zama sai dai a dakin ki, tun yanzu kina ruwan ido kowa ya zo kice ba kya sonsa, amma kuma kina son duk wani abu da zai 'kullo ya baki".

Mi'kewa ta yi bayan ta debi kunu da fanken tana cewa
"To Inna ai ba ro'konsu nake yi ba, Kuma Annabi yace ba kyau mai da hannun kyauta baya"

"Wannan maganar dai kin fi ri'keta a duk maganganun Annabi. saboda ta dace da ra'ayin ki, amma saka hijabi da ke yaci karo da tsarin ki, ai jiyan nan a gabana kika ce 'kauyanci ne"

Kasa magana tayi kawai ta shige 'dakinta, ta fara cin abincin ta, tana ayyanawa a zuciya duk saurayin da yayi gigin yi mata kyauta, ita ko ba zata 'ki amsa ba, tunda dai ba ro'kon su take yi ba.

Tana gama karyawa ta fita da kayan sannan ta sake yin brush wadda sau biyu take yi a kullum safiya tun Inna na mitar barnar makilin har ta gaji, ganin hakan yasa Baffa ya ware mata makilin din ta yana cewa uwar masu gida dole a bata komai, indai ba wadda ya wuce ka'ida bane.

Sai da ta shirya tsaf ta fito tana fadin Inna zan tafi, kallo daya ta mata taga yadda ta yi kyau tamkar ba uniform tasa ba, tasan 'yarta mai kyau ce fiye ma da Sumayya dan dai kawai ita duhun fatar mahaifin su ta kwaso amma Ubangiji ya mata cikkaken diri.

Ta nisa tace
"Iya! wannan turaren na ki bana zuwa makaranta bane,'kamshin sa bana shiga cikin maza bane".
 "To Inna" ta fada a gajarce ba dan ta gamsu ba.

" 'Daga can ki dauki kudin makarantar,yau Baffan ku jana'iza ya tafi tun sallar asuba bai dawo ba".

Turus tayi dan kuwa ba yadda za'ayi tasa hannun ta a wurin sana'ar Inna tunda ta riga ta shirya.

Ganin yadda taja ta coke tasan ta'bawa ne baza ta yi ba, kwafa tayi sannan ta mi'ke ta 'daga daron kayan, ta 'kirga kudin ta mi'ka mata, maimakon ta karba sai ta mi'ka mata pos din akan ta sa mata a ciki, hakanan tasa mata tana mata adduar shiriya, tun tana yar 'karamarta, bata son daddawa da kuka, da kubewa bushasshiya, da Inna ke 'kullawa tana siyarwa.

A bakin titi suka hadu da Zainab kamar kullum,suka rankaya suka tafi.
Suna Isa makarantar suka tarar da dodon na ta on duty, yana sizing kayan da makaranta ba ta yarda dasu ba.
Kowa yazo sai ya gaishe shi, hatta Zainab Ma'aji sai da ta risina ta gaida shi cike da girmama wa, amma ita banda kirne fuska ba abin da ta yi. kallo ya bi ta dashi yana raya wadda duk ke mata gugar kaya, ya kamata a bashi sarautar shugaban masu guga.
Ita ko sanin ba wani abu na karya doka a tare da ita yasa bata ji 'dar ba.
Har sun wuce sai yasa baki yace "Gogel"
Zuciyarta ta buga tare suka juyo da Zainab, amma sai yace Zainab ta tafi, itakuma ta dawo, tsaye ta yi mishi 'kerere fuskar nan tamkar gobara, ta gefen idonshi ya ke 'kare mata kallo baisan mai yasa kyaun da ta yi cikin sabon uniform 'dinta ya mintsine shi ba.

Sassanyan 'kamshin da ke tashi a jikin ta ya matu'kar ta'ba shi, ta na zuwa gaba daya gun ya cika da 'kamshi. ita kanta bata san tsadadden turare bane dan kuwa na Sumayya ne ta dauko mata.

Ba tare da ya kalle ta ba yace 
"On ur kneels"
Nan da nan hawaye ya cika idon ta wanne irin mugun mutum ne wannan? mai ta mishi zai wula'kantata daga dawowa? haka ta zube cikin 'kasa da ciyayi bai sallame ta ba, sai da ya tabbatar ta shiga sahun 'yan late comer's(makararru).
bayan ya mata bulala biyar a hannu masu zafin gaske, yana ce mata
" for ur indispline manners, u are not here only to learn, but da tarbiya in ganeral".
Haka nan dai aka sake mata punishment (horo)na latti. a wannan rana haka ta yini da ba'kinciki, murna da ake na shigar su aji shidda ita kuka ne ya maye gurbin, hankalin Khalil dana 'kawayen ta ya yi matu'kar tashi sai lallashinta suke.
dukkan su tsanar Mk ta cika 'kalbin su mussaman ma Khalil da ya ke jin tamkar ya yi hayar yara a bishi unguwar su a mishi dukan kawo wu'ka.





   Alkalamin 
SURAYYA DAHIRU
       ✍🏼✍🏼

Post a Comment (0)