HALIN YAU 21 & 22

🌺 *HALIN YAU*! 🌺


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•

   
      *SADAUKARWA GA*
      *SADIK ABUBAKAR*.




                  21_22.





Ranar da ya fara shiga ajin su a matsayin malamin harshen turanci(English language), ba abin da ya musu illah introduction, wato gabatar da kai,
ya sanar musu zai koyar dasu harshen turanci.

Bayan sun masa barka da zuwa, sai ya bu'kaci da kowannen su zai tashi ya gabatar da kan shi, as he did.

Sa'adatu da hankalin ta ya yi nisa wurin rubutawa Khalil Ibrahim reply din wasi'kar da ya mata na zai je School shop mai ta ke son ci?.

Ba ta san har anzo kan ta ba, sai da Halima tace "Gogel"!
Sannan ta yi firgit ta mi'ke, ba tare da ta rufe takardar da ta ke rubuta reply din ba, cike da yanga da iyayyi tace ,"I am Sa'adatu Bashir Gogel" daidai lokacin ya 'karaso jikin desk din na ta,
Yasa hannu ya na nazarin rubutun da ya 'dauke mata hankali, baice uffan ba ya dauki takarda ya zira a aljihun sa.

Wucewa ya yi yana fadin "next"
har aka kammala ya cinye period dinshi ya fice tare da takardar.
Takaici ya kama ta, ta fara tunanin mai ta rubuta ne?

_Nagode da kulawa Khalil komai ka ga ni indai ya burgeka, ni ma zai burgeni, Sa'a luvs you_.

Abin da ta rubuta kenan, haka kawai ta ji takaicin wannan Malamin da ya kira kanshi Mukhtar ya kama ta, Ina ruwan shi da ita daga zuwan shi?

Washa gari da ya shiga, karatu sosai ya zazzaga musu cikin turancin da ya kama bakin shi tamkar a 'kasar ingila ya girma.

Ya yi tambayar an fahimta ko da akwai mai tambaya?
Serious student din cikin su ne, su ka shiga tambayar abin da basu fahimta ba, shi kuma ya sake bayani a hankali dalla dalla, har kowa ya ce ya fahimta, sai yace zai yi tambaya.

Ba zato yayi pointing Sa'adatu Bashir ta tashi ta yi masa bayanin yadda ta fahimci topic din da ya gama bayanin sa.

Nan da nan taji ta muzan ta, saboda ba wani fahimta ta yi sosai ba, ta mi'ke ta na rarraba ido ta kasa furta kalma ko guda cikin tambayoyin da ya ke mata, da 'kyar tace "ban gane explanation din ba dama"
Ido ya zuba ma ta yace 
"We're not talking in Hausa but we're in English"
kunya ta kama ta, wato har ya gane ba ta iya mayar da magana da turanci? ya sake cewa "I ask all of you who didn't understand, but you mutter"!

Ita dai ba baki, sai ido tana jin wata kunya na kama ta. ya dade yana nazarin ta, sannan yace ta zauna ya sake bayani sosai, a lokacin kuma ta mai da hankali ta na sauraro tunda tana jin maganar, wurin mayar wa ne ke mata tasga'do.

Cikin 'kankanin lokaci ya fahimci ita da 'yan group din su, ba abin da suka sa gaba irin kwalliya da soyayya, mussaman idan class ba teacher to hirar kenan.
Transfer ta baza ta ce ta sami malaman makarantar, ciki har da class master din B class, na ss2 ajin su Sa'adatu, nan take kuma akasa Mukhtar Kabir Bichi a mastayin Class master din nasu.

Wannan damar da yasa mu ne ya 'kudure a ran shi sai ya canja wa'dannan daliban, abu na farko da ya yi musu ya rarraba musu gurin zama ya cillasu ta yadda sai dai hange a tsakanin su.

Haka kawai ya ji duk yafi jin haushin Sa'adatu saboda yadda ya lura wadda ta hada kai dasu din sun fita dama, kullum sai ya ga an kawo su a motoci masu kyau, an kuma zo an dauke su, sa'banin ita da ta ke zuwa da kanta cikin adaidaita sahu ko mashin,'kawarta da ya ke ganin suna zuwa tare Zainab Ma'aji sam ba halinsu 'daya ba, ba ta da hayaniya ta na kuma maida hankali wurin karatu duk da ita tana c class, ajin commercial.

Amma yayi nazarin sa ya gane buri da ra'ayin Sa'adatu ya kerewa mu'amala da irin su Zainab.

Saboda haka sai yafi matsa mata, kullum da kalar tambayar da zai mata, wadda kesa ta muzan ta.
Abin da ya lura dashi bawai 'ko'kari ne Sa'adatu ba ta da shi ba, illah mai da hankali ne ba ta yi.
sannan kuma tana da (infiority complex). ma'ana rashin 'kwarin guiwa akan kanka, tunda ya gane tsoron kar a mata dariya yasa ba ta son yin magana da turanci.

Wannan matsin da ya mata sai ya janyo tsanar shi a ranta, ta shiga fargaban zuwan period 'din shi,
a haka har akayi jarrabawar gwaji(Test). ganin a kowanne darasi bata ta'buka ko mai ba sai shiririta, sai ya canja salo ya fara disgata a gaban aji, ta hanyar 'kiran ta da sunaye kala kala, da suke nuni da ba abin da ta sani sai dai ta wanke uniform, ta yi yanga, amma empty brain, har cema ta yake bata dace da wannan makarantar ba.

Sannan kullum cikin bada misali da za'kwa'kuran dalibai masu azama yake, takaicin ta 'daya, yadda kullum misalin sa ba ya wuce da Farida Nasir Torodi , tun fil'azal ita jinin ta bai hadu da Farida ba, duk kuwa da ba ajin su 'daya ba,
Farida a A, science class kenan,
doguwa, siririya sosai, fara 'kal buzaye ne, gashin ta har gadon baya, farkon zuwan ta makaranta har nuna ta ake, na yadda ta ke tuma a cuci a kanta saboda idan ta tufke gashin yake girma, sai a hankali aka gane gashin ta ne.
Mai sanyin hali ce ko kadan ba ta da kwarafniya, bata kuma harkar 'kawaye.
'Kawar ta 'daya wadda kullum zaka gansu tare Ru'kayya mustapha.

Ga ilimi kamar me, dan kuwa tana cikin 'yan gaba gaba na 'dalibai masu haza'ka a duk fadin makarantar.

Sannan iyayen ta ma su wadata ne, domin mahaifin ta ambasadan Niger ne a Nigeria.

Wadannan abubuwan da Farida ta hada sai wasu cikin dalibai su ke mata kallon mai girman kai, da 'daukar ita wata ce yasa take ganin ta wuce kula su, shiyasa suma basa wani harka da ita ba ta da farin jini a tsakanin set dinta. barin ma da 4stars da suke ganin sai dai ta nuna musu kyan fuska amma ba dai na jiki ba😀.

Yawan misalin da yake yi da Farida ya 'kara tsanar ta a zuciyar Sa'adatu.

Cikin abubuwan da ba zata manta suba indan har za ta tuna rayuwar ta a FGC KANO, shine ranar da ya musu dictation wato yana fa'da suna rubutawa, ita kuma slow writer ce, kafin ta kammala rubuta wata kalmar, ya fadi ta gaba, kan dole ta ha'kura da bin, ashe yana lura da ita.
Sai da ya gama ta ji ya kira sunanta"Sa'adatu Bashir where's your note?"

Cikin daburcewa da tsoron yadda zai kunyata ta, murya na rawa ta tattaro kalaman da zai fahimce ta a gajarce ta ce
"My pen stop"
 
kafin ya yi magana anyi attishawa mai 'karfin gaske wadda ta iya shege ce, ba kowa bane illah Fahad Auwal! wadda shima haushin yadda ta za'bi Khalil ta barshi ne yasa yake jin da'din dizgin da ake mata.

Hannu ya mi'ka yana cewa "let me see"
zuciyarta ta buga amma hakan nan ta mi'ka mishi biron, ya duba ya ga lafiyar biro 'kalau ya watsa mata kallo tare da cewa "out of my class! I am tied of your manners" ta mi'ke sai kuma ta tsaya tace "Am sorry" cikin tsawa yace "don't sorry me, say sorry to ur parents who are keep westing their money".

Jin haka yasa ta fita, hawaye ya cika idonta, a baranda ta tsaya amma sai ya le'ka yace mata "on your kneels" kuka sosai ya kwace mata .
 
A ranta ta na tambayar kanta me ta mishi ne ya ke wula'kanta ta? mai yasa ya matsa mata? saboda ba ta da 'kokari ne dalilin? ta ke ta ji in dai 'ko'kari zai sa ta tsira da mutunci a idon wannan mutumin da ya yankewa tozarci cibiya to kuwa za ta nemo shi a ko'ina yake.

Sai da ya kammala darasinsa sannan ya fito ya kalleta yace "I want you to borrow your boyfriend's note, and copy what you can't write by urself, if not u will be in.." ya girgiza kan shi ba tare da ya fadi mai zai biyo baya ba .

Ya wuce ta yana sa ke fadin "useless girl, you can go back to ur class".

Tsawon lokaci ta shafe a gun tana kuka tsabar ba'kin ciki zuciyarta Kamar ta fashe, har sai da ta hango Mr uche's wadda ya ke 'daukan su darasin tsumi da tanadi(economics). sannan ta mik'e ta na kar ka'de jikin ta, ta shige ajin ta na ganin wa'danda dama su na jin haushin su, ita da 'yan group din su, su na bin ta da wani irin kallo, mai kama da madallah.




AL'KALAMIN
SURAYYA DAHIRU
     ✍️✍️.

Post a Comment (0)