33. HUKUNCIN AUREN HANNU
Tambaya:
Assalamu alaikum, Malam menene hukuncin masturbation (Istimna'i) a Musulunci?
Amsa:
Wa alaikum assalam. To, ƴar'uwa babu nassi ingantacce bayyananne yankakke da yake haramta wasa da al'aura har maniyyi ya fito, duk hadisan da suka zo ba su inganta ba, sai dai wasu Malaman sun haramta auran hannu saboda aya ta (6) a Suratul Mu'uminun ta iyakance biyan bukata ta hanyar matar aure ko bayi kawai, wannan sai ya nuna abin da ba wadannan ba ba'a iya biyan bukata ta hanyar su.
Yin wasa da al'aura har maniyyi ya fita yana haddasa matsaloli a likitance. Sai dai, yana daga cikin ka'idojin shari'a idan cututtuka biyu suka hadu ya zama babu yadda za ayi sai an aikata daya daga ciki sai a zabi karama a aikata, wannan yasa Imamu Ahmad da Ibnu Hazm suka halatta auran hannu ga wanda yaji tsoron zina kuma ba shi da halin da zai yi aure.
Auran hannu haramun ne, sai dai ɓarnar dake cikin zina ta fi girma, domin zina akwai keta alfarma a ciki, sannan tana kaiwa ga cakuduwar nasaba, ta yadda za'a haifi ƴaƴa gantalallu marasa asali, wannan yasa magana ta biyu ita ce mafi inganci, mutukar an samu sharuɗan da suka gabata.
```Duba: Muhallah 12/407 da Majma'ul Fataawaa 34/146.```
Allah ne Mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.