HUKUNCIN AZUMIN SITTU SHAWWAL 6⃣
Arubutu na biyar mun tsaya akan ambato wata magana ta imam malik na cewa baiga wani daga cikin malamai yana azumtar wannan azumin ba, wanda kuma mun bada amsa akai, wanda awannan rubutun zamu anbaci shin ko imam malik yana yin wannan azumin??
📝 SHIN IMAM MALIK YA KASANCE YANA AZUMIN SITTU SHAWWAL??
Wannan tambaya ce da dayawa daga cikin mutane da zasu raya azuci cewa kamar zasu iya bada amsarta bisa ga la'akari da maganansa da ta gabata da kuma ta'aliqin wasu malamai na malikiyan, mai karatu zai iya cewa imam malik bayayi bisa ga dogaro da wancan dalilan, to amma bari muji amsar wannan tambaya daga bakin daya daga cikin manyan daliban imam malik, wanda ya zauna tareda imam malik tsawon shekara goma sha bakwai (17years), wato *MUDARRIF*
Mudarrif Allah ya masa rahama yake cewa "Imam Malik ya kasance yana azumin sittu shawwal saboda abunda aka ruwaito na falala da wannan azumin yake dashi, amma imam malik baya bayyana wa gama garin mutane saboda tsoron abunda aka ambata".
Sannan ya cigaba da cewa "Imam malik ya kasance yana azumtar wannan azumin aboye, kawai ya karhanta wannan azumin ne saboda gudun kada jahilai su hadashi da ramadhan, amma duk wanda zaiyi saboda kwadayin ladan da yazo dashi to wannan imam malik bai hanashi ba".
النوادر ٢/٦٢، شرح الزرقاني على الموطأ ٢/٢٠٣، حاشية الدسوقي ٢/١٤١، المنتقي ٣/٩٢، المفهم ٣/٢٣٨، تهذيب السنن ٣/١٢١.
📖 WAYE MUDARRIF??
shine Mudarrif bin Abdillah bin mudarrif bin sulaiman bin yasaar Alyasaaril hilaali. An haifeshi a shekara ta 139 ko 140 bayan hijira, ya mutu a shekara ta 220 bayan hijira.
Yayi ruwaya daga imam malik da Ibnu Abiz zinaad da Ibnu Abil mawali da kuma Abdullah bin Umar Alumari.
Cikin wanda suka ruwaito daga gareshi akwai; Abu hatim, Abu zur'a, Ibrahim binul munzir, zuhali, Yaqub bin shaiba, da imamul bukhari.
Mudarrif ya kasance shine kan gaba cikin daliban imam malik gabadayansu, kamar yadda imam Ahmad Allah ya masa rahama yake fada. Babu wanda ya raunana shi cikin malaman jarhu wat ta'adil banda Ibnu Adiy, shima kuma sauran malamai basu yarda da jarhin nasaba kamar yadda Alhafiz Ibnu hajar yake fada.
طبقات ابن سعد ٥/٥٣٨، ترتيب المدارك ١/٤٧٩، تقريب التهذيب ٢/٢٦٠
Munkawo wannan takaitacciyar tarjama ta shine saboda dalilai guda biyu;
1. Bayyana wa mutane wanene shi wannan mudarrif din, shin za'a iya daukan maganan sa akan imam malik ko baza'a iyaba?? Wanda wannan amsar mun same ta acikin jawaban da muka gabatar.
2. Nusantar da mai karatu akan wana mudarrif muke nufi, kasancewar guda biyune da suka shahara, dayan tabi'ine mudarrif Bin Abdillah bin shakheer wanda ya mutu a shekara ta 95 bayan hijira.
Arubutu na gaba in sha Allah zamu tashi akan wasu daga cikin mas'aloli da suka shafi wannan azumin na sittu shawwal.
Julaibeeb
9/10/1441
1/6/2020
#zaurenfisabilillah
https://t.me/Fisabilillaaah