TSAKANIN SO DA SOYAYYA // 06

TSAKANIN SO DA SOYAYYA // 06


Muna ta qoqarin rabe tsakanin sha'awa ne da soyayya ta gaskiya, wasu suna ganin soyayya kafin aure gaskiya ce, kalmar "sha'awa" da muke sakawa kuwa fahimtarmu ce kawai, ba dole ne ta zama hakan ba, to don rabe dan kuka da dan tsamiya bari mu ga abin da ke faruwa, shin sha'awa ce ko kuwa soyayyar gaskiya ce?

Mace, wace ta san namiji zai zo wurinta zance, takan gyara kanta ne sosai, in ma ba ta yi hakan ba, mahaifiyarta za ta yi mata fada, (A wayewar yau kenan), za ta yi wanka, ta caba ado mai ban sha'awa da daukar rai, ta fesa turare, ta zuba kaya masu kyau da fisgar idanun namiji, ta gwamatsu da shi, tana magana da shi cikin sanyin murya, dan abu kadan ta yi dariya, sannan a cikin duhun dare, ba kowa tare da su sai shedan wanda fatarsa ya ga ya dasa sha'awa mai qarfin gaske a zukatansu.

Shi kuwa malam Zurqe, bai fito ba sai da ya qure adaka, ya kamfato masu gidan rana ya watsa a aljihu, ga turare mai fisgo hankali ya fesa, shi ma ya gwamu da ita, da ta dan yi shuru ya ce "Mene ne?" wato a dole shi mai kula da ita ne, qoqarinsa ya mallaki tunaninta, ya figi hankalinta, ga kuma shedan yana ta agaza masa, yana daure tsakanin zuciyoyinsu, yadda ko da zai yi mata abin da ba ta so, ba za ta iya yi masa magana ba, tana tsoron kar hankalinsa ya baci, ta zo ta yi asarar irin soyayyar da take tsammanin ta gaskiya ce, a duk wadannan abubuwan in ban da kusantar saduwa meye sakamakon abin da suke yi?

To ya kuke gani in da sun zauna ne da rana nesa da juna a dakin mahaifiyarta ido na ganin ido, mutane suna shiga suna fita, ga yara suna wasansu? In fa zai shiga gidan zance akwai wasu abubuwa da su kansu ma'auratan za su amfana, shi dai zai saba da mutanen gidan, don in shi ba bangare ne nasu ba ba yadda za a yi qato kamarsa ya shige dakin matar aure, ko turakar mijinta, sannan ban da haka ma zai ga yadda tarbiyyar gidan take, ta nan zai ga yadda zai tafiyar da iyalin tasa in ta shigo gidansa.

Ita kuwa yarinyar za ta fi kowa amfana da haka, domin har gidansu yake shugowa, dole dai ya ga qimar iyayenta kafin ya sami damar zama tare da ita a cikin gida, wannan damar kuwa ba za ta taba samuwa ba sai an yi magana ta baka da baka tsakanin iyayensa da na ta, kenan maganar tsilla-tsilla ko ban shirya ba ba ta ma taso ba, ya riga ya kamu ba sauran yaudara, saura maganar aure kawai wace shigowarsa za ta sa ya dago maganar da wuri, ko iyayenta su tursasa ta ta yi masa magana, don kar a wuce makidi da rawa.

Kasancewarsu a cikin gida, kuma a gaban iyaye dole maganganunsu su zama bisa tsari, ba na sha'awa da za ka ji yana cewa in bai gan ta ba ba zai sami wata natsuwa ba, ita kuma ta yi murmushi ta saukar da murya "Wallahi ni ma haka!" Kuma tabbas haka din ne, shi ya sa don ta saba wa iyayeta a kansa ko ta ba shi duk abin da yake so ba wata matsala ba ce.

To amma da a ce yana jawo hakalinta ne bisa ikhlasi, da bin iyaye, da fadin gaskiya da amana, domin gyara irin rayuwar da za a yi nan gaba, ita kuma tana masa wasu 'yan tambayoyi a kan rayuwarsa don sanin yadda za ta zauna da shi, tana jawo hankalinsa game da zumuntarsa, wato alaqarsa da iyayensa da kuma sauran 'yan uwansa, da wahala ka ga yawan shiga da fita ko yuwuwar saba wa iyaye ko wuce gona da iri kafin aure, kuma a wadan nan yanayi guda biyu ne zamu gane wanne ne ginin soyayya mai dorewa.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)