KADA KU TAƘAITA DA HADDATAR DA YARA ALQUR'ANI KAƊAI, KU HAƊA MUSU DA ILMIN HADISI DA FIQHU

KADA KU TAƘAITA DA HADDATAR DA YARA ALQUR'ANI KAƊAI, KU HAƊA MUSU DA ILMIN HADISI DA FIQHU


Sahabi Huzaifa bin Al-Yamaani Allah ya ƙara masa yarda yake cewa; Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce: "Lalle yana daga cikin abinda nafi ji muku tsoro shi ne; wani mutum da zai karanta Alqur'ani ya haddace shi, har takai ga ana ganin alamun karatun ajikinsa (ana ganin alamun tsoron Allah, da ƙanƙan da kai atattare dashi) kuma ya kasance mai bawa musulunci da musulmai kariya,(yana ƙoƙarin karantar da Alqur'anin) amma sai ya watsar da Alqur'anin ya jefar dashi a bayansa ya je ya ɗauki takobi ya yaƙi maƙwabcinsa yana mai jifansa da kalmar shirka (yana cewa jinin maƙwabcin ya halasta domin ya bar Musulunci yayi shirka).
   Sai Sahabi Huzaifa ya ce ya manzon Allah waye acikin su yafi cancanta da shirkar?? Wanda aka jefa da kalmar ko kuma wanda yayi jifan?? Sai Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce "a'a wanda yayi jifan dai, shi ne yafi cancanta da zama mushrikin).
السلسلة الصحيحة ٣٢٠١

#Zaurenfisabilillah 

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)