26. TA AURI WADDA BA YA IYA JIMA'I HAR SUKA RABU, SHIN ZA TA YI IDDA?
Tambaya:
Assalamu Alaikum malam, wani bawan Allah ne ya auri ƙanwata, sai daga baya muka gane ya ha'ince mu sakamakon rashin mazantaka da ba ya dashi, daga baya da asirinsa ya tonu sai ya sake ta, shin malam zata yi idda ne? Don babu wata mu'amalar aure da ta taɓa shiga tsakaninsu.
Amsa:
Wa alaikum assalam, mutuƙar ba su taɓa kwanciyar aure ba, ai babu idda akanta, kamar yadda aya ta (49) a Suratul Ahzab ta yi bayanin hakan, amma in har yankar kaciyarsa ya ɓuya a farjinta ya wajaba tayi idda, zai yi kyau kuje wajen Alƙali saboda ya tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.
Allah ne mafi sani.
Amsa daga Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.