YA HALASTA INCI ABINCI A GIDAN TA’AZIYYA?

YA HALASTA INCI ABINCI A GIDAN TA’AZIYYA?
:


*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum, mal menene hukuncin wanda ya ci abinci a gidan ta’aziyya. Abincin da ake rabawa yan zaman makoki, ya halatta aci ?
:
*AMSA*👇
:
Wa’alaykumussalam, 
Abinda sunnah ta tabbatar shine makwafta su dafa abinci su kai gidan da akayi rasuwa kamar yadda Hadisi ya zo cikin sunan “Attirmizy 998 da sunan abu dauda 3132” hadisin Ja’afar ibn Abi dhalib, 

Hakanan imam Shafi’i a cikin littafin sa” Al’ummi 1/317” shima ya tabbatar da haka.

Jamhurun malamai sunce makaruhi (Abin kyama/ki) raba abinci ga wadanda sukazo ta’aziyya wasu ma sunce bidi’a ne yin hakan kamar yadda ya zo cikin “Fathul ƙadeer 2/142”

Babban malamin a mazhabar Malikiyya imam Alhaddabi Almaliki yace cikin sharhin muktasar kaleel wato mawahibul jaleel 2/228 makaruhi ne rabawa masu ta’aziyya abinci don ana kirga hakan cikin bidi’a. Hakanan Sheikhul Islam ibn taymiyya a cikin fatawar sa 24/316 yace taron mutane a gidan mamaci da raba abinci a ci wannan bidi’a ne ya kawo maganar jareer ibn Abdullahi cewa mukan dauki taron jama’a da raba abinci a gidan mamaci a zamanin mazon Allah a matsayin `Niyaha’ wato shelar mutuwa irin wanda shari’a ta hramta.

Wallahu A’alam.

*Malam Nuruddeen Muhammad (Mujaheed)*

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)