WASU MATAN // 04

WASU MATAN // 04


A gafarcemu munyi missing rubutu na 3🙏🏻🙏🏻
.
Ita wannan ta sami matsala ne tun tuna budurwa, yadda shedan ya ribace su ita da saurayin har ya qunsa mata ciki kafin ta bar gidansu, ta yi ta boyewa, kullum tana cikin wahala amma ba damar ta fada.
.
A haka har aka daura aurenta da saurayin, sai dai su biyun ba su aminta da cikin ba, suka yi qoqarin zubar da shi duk da cewa ya kai wata 6, nan ma ta kusa rasa ranta, aka kwashe ta buuuu! Sai asibiti, da yake tana da sauran numfashi aka shawo kan lamarin da qyar.
.
Yarinya ta dawo gida, uwayen suka matsa kan cewa ba za ta koma gidan mijin ba saboda tunanin cewa wulaqanta ta zai yi, ba zai ga mutuncinta ba.
.
Ta nace kan cewa in dai ba shi ba to sai dai ta bazama karuwanci ko ta rasa ranta, kuma za ta iya din tunda za ta kalli tsabar idun uwayen ta fadi abinda take so, a dole dai suka saduda suka qyale ta ta koma, shuru dai ba wani mai jin komai, ashe haquri take yi da shi don ba inda za ta kai kuka, wulaqancin yau daban na gobe daban, in ya dan yi shaye-shayensa ya zo ya huce a kanta.
.
Babban abin baqin-ciki a ciki shi ne ba a san iya sakin da ya yi mata ba, har dai uwayen suka ga lallai barinta da shi ba zai sa ta yi la'asar ko ta fahimci cewa Borno gabas take ba, su ma sunansu baci kawai zai yi, suka yi gaban kansu suka dawo da ita gida da qarfin tuwo.
.
Ita kuma da ta tashi zuwa ta kwaso diyoyinta ta dawo gida, maigidan ya biyo sawu ya qwace yaransa, bisa hujjar cewa kowa ya tsaya a gidan ubansa, bayan kwana biyu ita ma ta yi batar dabo, ko sama ko qasa.
.
Bayan bincike me zurfi sai aka gano cewa ai binsa ta yi, sun bar yaran a kula musu da su suka qara mai, irin wadannan matan a wani aji za ka saka su, ba shakka uwaye na qoqari, matan na jin zafin abin da ake musu, amma ba sa iya tunanin abubuwan da za su biyo baya tare da qaruwar shekaru.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)