BEGENKI
Begenki yana a raina
Ke ce jinin jikina
Sannunki ruhina
Sanyin idanuna
Zaƙi nq bakina
Sirrin muradaina
Na fahimci so da ƙauna ne akanki
Na san ƙuna da da jin daɗi akanki
Zuciyata ta fara bugawa ne akanki
Na yi dungure da kodumo akanki
Zuciya tana ta ƙorafin ƙaunarki
Ƙwaƙwalwata tana ta begenki
Zan iya kuka akanki
Zan iya hauka akanki
Na yi maye ma akanki
Na yi tamɓele akanki
Na yi tsalle akanki
Zan iya naushi akanki
Bishiyar begenki ta yi fure waye zai tsinko ki
Kogin begenki na faɗa na yi yo nutso akanki
Rawar ƙauna na taka duk domin a yabe ki
Littafin so zana rubutu saboda duniya ta fahimce ki
Ita rayuwa bata da ma'ana in har ba ƙaunarki
Ban son iska ko abinci ma sai dai in ta kallon ki
Idanuwan ki
Laɓɓanki
Kumatunki
'Yan tsunki
Gashin kanki
Da komai naki
Ni talaka ne ba shakka in har na rasa ki
Bani da komai koda kuwa zan kwana a banki
Tajiri ne ni matuƙar za a ce in same ki
Ko Ƙaruna a wurina ba shi min gorin arziƙi
Dare da rana bani da aiki sai dai begenki
Idaniya har ƙosawa suke ta yi da su kalle ki
Su kalle ki
Zuciya ta gane ki
Hanci ya ji ƙamshinnki
Kunnuwa su ji muryar ki
Ƙwaƙwalwa ta bar begenki
Ruhi ya same ki
Ga saƙona da fatan dai zai same ki
In ya iso to ki sani ina ƙaunarki
Sannan zuciyata tana mararinki
Kuma ko da yaushe ina begenki
Rayuwata dukkanta na baki
In ma kin so ki yar kawai ki wuce abin ki
Hmmmmm
Ƙaunarki
Mararinki
Muradinki
Fatan auren ki
Begenki
Ina Begenki
✍🏻 Jamilu Abdulrahman
( Haiman Raees)
Haimanraees@gmail.com