DAMINA
Yabanya ta yi shar-shar
Furanni sun yi luf-luf
Damina ta kankama
Muna godiya wurin sarki
Bismillah da kai zan fara
Abin bauta wurin kowa
A duk lamura in zan fara
Zan fara ne da mai kowa
Allahu da shi ya yi Ɓera
Ya yo Akuya yayo Shirwa
Ya aiko Manzon tsira
Da saƙo bai ɓoye ba
Tsira da aminci mai girma
Ka yi wa ɗaha mai baiwa
Da su ahalin gidan girma
Sunan ku ba za na manta ba
Sahabban nan masu girma
Ko ɗai fa ba za na manta ba
Tabi'ai har da ku Ulama
Ƙaunarku ba za na daina ba
Yau ruwa na ta sakkowa
Damina ta kankama
Iskar damina na ta kaɗawa
Tana ta kiran masu noma
Hatsin ku kuyo shukawa
Domin yau ba batu na zama
'Yan dashe ku yi dasawa
Masu noma ku yo noma
Samari a bar zaman banza
Mu ɗau noma akwai riba
Masarar ga da zarar tai geza
Kulata ba za mu kasa ba
Mu samu kuɗi mu yo hidima
Mu bar kallon abin kowa
Albarkar da ke cikin noma
Ba shamaki wurin kowa
Mu shuka gyaɗa ko dauro
Mu dasa rake ko yalo
Ga masara ga iburo
Ga dankali ga dawa
Ga masara ga shinkafa
Ga rogo nan kuma ga saura
Shi noma bai da iyaka
Noma shi ne jigon talaka
Kana iya duƙawa ka yi
Kana iya sa wasu su yi
Kana iya biya ma a yi
Kana iya cewa zo mu yi
In dai da hali je ka yi
Ko da kaɗan ne je ka yi
In dai ko har ka yi
Jin daɗi tabbas za ka yi
Kana iya yi domin ka ci
Kana iya yi ka kai shi gida
Kana iya yi wasu su ci
Kana iya yi ka kai kasuwa
Kana iya yi don nishaɗi
Kana iya yi domin tari
Kana iya yi domin aure
Kana iya yi don wata rana
Allahu ka dubi bayinka
Da ke noma cikin gona
Ka sa musu albarka
Cikin noma a can gona
Da sun duƙa za su yi shuka
Ka sa ta fito cikin gona
Ka ba su tsaro da ƙarfinka
Dare rana cikin gona
✍🏻 Jamilu Abdulrahman
( Haiman Raees)
Haimanraees@gmail.com