HALAYEN DA AKE SO MACE TA GARI TA KASANCE DASU

HALAYEN DA AKE SO MACE TA GARI TA KASANCE DASU



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum malam barka da rana ya kokari da Kuma iyali ALLAH ya taimaka malam Dan ALLAH waɗanne halayene akeso mace ta gari ta kasance dasu?
Kuma Nima zan iya shiga cikin mata na gari wadanda ALLAH ya ambata a cikin alqur'ani Mai girma ALLAH ya baka ikon ansaman tambayata ngd.
:
*AMSA*👇
:
Allah Ya Ambaci Mace ta Gari a Cikin Alqur'ani Mai Girma Inda Yace SALIHA, MAI TSORON ALLAH, MAI KIYAYE KANTA KODA MIJINTA BAYA NAN, NA DAGA ABINDA ALLAH YA BATA UMARNI DA TA KIYAYE.

 Mace ta Gari itace Mai Hakuri, Mai Ganin Girman Mijinta da Girman Iyayensa. Domin Ta sani Iyayensa ne suka Haifa Mata shi. Ba itace ya Haifa Musu Shi ba. Wanda sa Ace basu Haife shi ba. Ita ba zata same shi ba. Kuma ba zata taba Haihuwarsa ba. Domin Mace Bata Haifarwa Kanta Mijin da zata Aura.

 Ina ganin Shirmen Wasu Matan da suke Rigima da Iyayen Mijinta. Wani Lokacin shi Kuma Mijin sai ya Goya Mata baya. Su Haɗu Shi da ita su Wulakanta Iyayensa. Wanda Wallahi Ita ba zata taɓa Yarda shi da Ita su Wulakanta Iyayenta ba. Duk da Cewar Wani Lokacin Ma Asiri Suke Yiwa Mazan Nasu.

 Mace Ta Gari Itace Wadda Idan Iyayenta Suka Gaya Mata Magana, Take Kallon Wannan Maganar ta Mahaifanta fiye da Zugar kawarta ko wata mata ta daban.
  Itace Wadda take girmama Mijinta Fiye da Kowanne Mutum a Faɗin Duniyar Nan.

 Mace ta Gari. Tana da kawaici da Bin Komi a Sannu a Sannu. Bata Tayar da Fitina. Bata Daga Murya Akan Mijinta ko Yayansa ko kuma Kishiyarta. A koda Yaushe Fatanta a Zauna Lafiya.

 Mace ta Gari, Itace Mai Kiyaye Adonta, har sai ga Mijinta Shi Kadai. Itace mai Zama a gida, bata Fita daga Gidan Aurenta. Har sai da Wani dalili na Shari'a, Bata Fita Har sai da Izinin Mijinta. Kuma inda ta Tambaya Iya Nan zata je ta dawo. Ba tare da ta Shiga Wani Wuri na daban Ba.

Mace Ta Gari Itace Wadda take Bibiyar Abinda yazo Mata. Ba Neman Labarin da Bai zo mata ba. Kuma Tana Aiki da Kyakykawan Labari ne kawai. Maras kyau. Zata kawar da kanta Akansa.

 Mace ta Gari. Itace mai Yawan godiya Ga Mijinta a Daidai Lokacin da yayi Mata Alkairi. Ko ya yiwa wani Nata Alkairi ko kyautatawa.

 Mace ta gari. Bata Sabawa Allah tana sane. Har sai idan a bisa kuskure. Kuma a duk Lokacin da ta Saɓawa Allah, zaka same ta tana yawan Tuba Ya Zuwa Gare Shi.

 Haka Zalika Mace ta Gari, duk Lokacin da ta Saɓawa Mijinta, tana Gaggauta Neman yafiyar sa. Bata Iya Barci, har sai idan yayafe mata. Sannan Ne zata sami Nutsuwa.

 Mace ta Gari. Kome ta samu. Bata Sarrafa shi, sai Abinda Mijinta Yace Shi zata yi.

 Mace ta Gari, bata Takura Wa Mijinta sai yayi Mata Abinda bashi da Ikon yimata shi.

Allah Shine Masani.

✍️
ZAUREN FADAKARWA A SUNNAH MAZA MATA 08137783797

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
KU BIYOMU A WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)