KISSAR "BARIRA" GAME DA AUREN DOLE GA IYAYE

KISSAR "BARIRA" GAME DA AUREN DOLE GA IYAYE


:
https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf
:
*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum
Barka da yau malam dafatan kana lapiya Allah yasa haka Ameeeen Allah yakara ilimin me amfani.
       Malam tambaya nakedashi shin malam akwai matarda azamanin annabi takashe aurenta saboda batason mijinta haryadinga binta yanamata Waka saboda matsananciyar kaunarda yakemata
  Shin malam wannar matar tashiga aljanna kuwa kokuma ince tayi aikin da daga baya yakaita aljanna
:
*AMSA*👇
:
Wa Alaikis Salaam:-
 Ni ban San wannan ba. Abun da ya zo a Hadisin shine, *_BARIRA_* ita Kungace ta Nana Aisha Allah ya Kara Yarda Gare ta, Sunan Mijin ta *_MUGIB_* ta rabu da Mijin ta, Sai Mijin Nana Kuma Allah ya sanya Masa son ta fiye da yadda ba'a Tsammani itama Kuma tana da matukar Qin sa ba ta Son Shi. Idan ta zo wucewa toh zai Yi ta bin bayan ta a cikin Madinah har sai ta mule ya koma. 

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihin Wasalam, Kuma Yana Tausayawa irin wannan Soyayyar, toh abun ya dame shi, domin Annabi ya ga masoya Sun Shaku Sosai Sai Annabi yace Ina ma ga Auren Suka Yi, Manzon Allah ya kalla ABDULLAHI Dan Abbas yace Shin ba ka jin Tausayin MUGIB sabida irin tsananin So da Beje da yake yiwa Barira Kuma ba ka Mamakin Yadda ita BARIRA take Tsananin Qin Sa ba ta Son Sa? Yace Na'am Ya Rusullahi Wallahi Ina Mamaki.

A Karshe aka Nemi Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasalam ya Sanya Baki Akan wannan Matsalar nasu BARIRA da Mijin ta, Sai Annabi ya tashi da Kansa da Kafafun sa ya je ya samu ita *_BARARI_*, bayan Sun gaisa Sai Annabi yace Barira Ki Yarda Ki Amince MUGIB ya sake Auren ki? Wato ya sake Daura mata Aure!.

Sai wannan Matar *_BARIRA_* take Cewa Manzon Allah, Shin Shawara Kake Bani ne, Ko Kuma Umarni Kake Bani? Sai Annabi yace mata ah ni Shawara nake ba ki. Sai wannan Matar Barira take Cewa Annabi toh Ni bana Son Sa ba zan taba komai gidan wannan mutumin ba.

Abun da take Nufi Shine, tace in da Umarni kake bani Wajibi ne dole ne Na bi a Matsayin ka na Annabi, Amma tunda Shawara ce toh Ni bana Son Sa Ba zai Koma Gidan Sa ba. Haka Manzon Allah ya tashi ya fita ya koma gida ba tare da ta Amince da abun da ya zo mata da shi ba.

Abun da Malamai Suke Cewa anan Shine, Inda Ace Annabi yace Mata umarni yake Bata, da Wajibi ne ta bi umarnin Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasalam idan ta Qi bin Umarnin Manzon Allah, Toh ta Kafirta Babu ita Babu Shiga Aljannah. Amma sai Annabi yayi mata Adalci Daman shi Mai Tausayi ne da Adalci ga Mutane shine yace Mata A'a Shi Shawara yake Bata bawai Umarni ba.

Shiyasa Malamai suke Cewa idan ikon da ƊA ne Ko Ɗiya ko Baban ki Wadda ya Haife ki ne Bai Kai Annabi ba, Manzon Allah shine yafi Cancanta da ya TILASTAWA wata Mace Musamman ita BARIRA ta Auri MUGIB tayi Auren dole, Auren Mijin da ita ba so, Amma Annabi ya Bawa Wannan Matar BARIRA Zabi Bai CE Umarni ba, Shiyasa ake Cewa Bai halatta ga Uba ya TILASTAWA Ɗiyar sa Auren Wadda ita Bata Son Shi ba, Idan yayi hakan ya Saɓawa Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihin Wasalam. Domin ga Annabi Yana da ikon ya TILASTAWA wannan Matar BARIRA ta sake Auren Tsohon Mijin ta domin ga irin Wahalar da yake Sha Akan Son ta, Amma Annabi Ya Qi ya TILASTA mata duk da Wahalar da Mijin yake sha.

Da wannan ne Malamai Suke idan An yiwa Mace Auren Dole kina da ikon Ki Raba Wannan Auren domin kene za ki je ki Zauna a gidan Mijin bawai Sune za su zauna Miki a gidan Mijin ba, don Haka za ki nemi Waliyyan ku ayi maganar Fahimta ku rabu, idan sun gagara Sai a samu Alkali Masanin Shari'ar Musulunci shi ya San me Hukuncin Auren ku. 

Idan Kuma Shi Mijin Mutumin Kirki ne, ya Cika Sharruda ta yadda duk inda ya je Neman Aure Za'a iya ba shi Auren Mace, Mijin Yana da Addini da tsoron Allah da Adalci ya San Yakamata Salihin Bawa ne Mai hankali Halayyen sa da Dabi'un sa duk Babu Abun Yarwa, toh Shawarar Shine ki So shi, So na Tsakanin da Allah Kamar yadda shima yake son ki. Idan kin Yi kin Yi Son Sa ya gagara Shiga Zuciyar ki, toh kada Zama da shi ya Kai ki Saɓawa Allah sai ku rabu.
Idan ba mutumin kirki bane, Bai da Addini Halayyen sa ba Nagari bane, idan ya je Neman Aure a wani gurin Za'a Hana shi, toh ki bi Matakin can domin Rabuwa da shi.

 Sabida Haka wannan shine abun da ya zo a Shari'a da Hadisi. Amma bawai Matar da ta Kashe Auren ta bayan Haka Kuma Wai ta zo tayi Aikin Aljannah ne ko kuwa?. Ni ban San wancan Maganar ba. Abun da na sani kenan shine bayanin da na kawo Miki. Fatan kin gane?

Wallahu A'alamu.

*_MUHAMMAD TUKUR JALINGO_*

GROUP ADMIN:👇
Mal. Khamis Yusuf
+2348087788208
+2348054836621

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)