INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA HALATTA A SHARI'ANCE?

INA YAWAN WAYA DA BURDURWATA, KO YA HALATTA A SHARI'ANCE?

                           TAMBAYA❓


Dan Allah ina tambaya. Namiji ne yakeso ya qara aure to shine bayan ya dawo gida da dare sai budurwar ta riqa kiran shi ko kuma ta riqa turo txt, shikuma idan matarshi tana kusa sai ya riqa avoiding amma data dan daga sai shima ya fara responding, ko ya kira ta kuma idan asuba tayi sai ta kirashi. To shine matar ba taso, dan Allah a Shari'ance yanada laifi ko ba shi da? sannan matar zata iya neman ya dena ko kuwa ta shiga rayuwarsa ne a shari'ance?

                               AMSA👇

To dan'uwa yana da kyau ka san cewa matar da kake nema aure ba muharramarka ba ce, don haka bai halatta ka dinga hira da ita ba, sai gwargwadon bukata. Yawan hira da budurwa da jin dadin zancenta, yana daga cikin abubuwan da suke kaiwa zuwa ga fitina, mai AHLARI ya kirga jin dadin zancen wacce ba muharrama ba daga cikin ayyukan da Allah ya hana. Duk wanda yake yawan hira da matar da ba muharramarsa ba, yana jin dadin zancenta, Allah zai iya haramta masa jin dadin zancen matarsa ta halal.

Ya wajaba hirarka da buduwarka ta zama gwargwadon bukata, saboda jin dadin zancenta, zai iya kai ku ku aikata katon sabo, yana daga cikin ka'idojin shari'a toshe duk hanyar da take kaiwa zuwa barna.

Zunubi shi ne abin da ya sosu a ranka kuma ka ji tsoron kar mutane su yi tsinkayo, kamar yadda hakan ya tabbata a hadisin Muslim mai lamba ta: 2553.

Allah ne mafi sani.

Amsawa:- Dr. Jamilu Zarewa.
Post a Comment (0)