JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 12
.
QISSOSHIN BANU ISRA'ILA
Idan ka bi tarihin banu Isra'ila da aka ciro a littafansu za ka taras ba wani annabin da suka qyale shi ba su tabi mutuncinsa ba, sun mayar da su ba ma'asumai ba, da kamata ya yi mu koyi darasi da dama cikin tarihohinsu ba mu qarar da lokacimmu wurin karanta qarairayin da suka kawo a littafansu ba, yanzu dai bari mu karanci wasu abubuwa a kan qissar Daluta da Jaluta:-
1) Duk wata al'ummar da aka danqwafe ta aka qwace mata haqqinta aka wargazata zai yi wahala ta koma ta kwanta, za ta fara tunanin abinda aka yi mata ne ta sake wani shiri na dawowa a matsayinta na farko.
.
Wannan shi ne abinda ya faru da banu Isra'ila lokacin da aka kore su daga Palestine, sai suka fara neman wanda zai hada kansu su koma matsuguninsu na farko.
2) Duk yadda al'umma ta lalace sai ka sami daidaiku wadanda qwaqwalwarsu ke kawo wuta, su za su yi tunanin mafita su gaya wa sauran, ai banu Isra'ilan ne da kansu suka nemi Daluta da ya kawo musu sarki, sun gano cewa wannan ne kawai zai iya zama mafita garesu gaba daya.
3) Duk yadda manya masu fadi a ji na al'umma suka yi tunanin mafita suka gaya wa mabiyansu ba za a taba cin nasra ba sai sun fito da gaske sun sa hannu wurin kawo sauyi a aikace, surutu a baki ba mafita ba ne.
.
4) Samun sabani wurin zabin shugaba, wannan sunnar rayuwa ce ba yadda za a yi da ita, sai dai akwai buqatar samun wani tsayayye a tsakiya wanda zai tilasta yarda da wanda ya fi, kamar yadda banu Isra'ila a qarshe suka dauki Daluta tare da hukuncin annabin wannan lokacin.
5) Da wahala a ce mutane sun gamsu -wajen zabin shugaba- da abinda ya saba wa buqatunsu, duk abin da ba zai yi musu hidima ba suna iya tunkude shi cikin sauqi, banu Isra'ila ne da kansu suka nemi a samar musu da jagora, amma sun qi shi ne don ba a cikinsu yake ba kuma ya bayyana musu cewa ba mai arziqi ba ne.
.
6) Tunanin al'umma kan karkata ne wurin cewa wanda bai da dukiya bai dace ba ya shugabance ta, ko yanzu za ka taras sai an yanki tikiti da kudi mai yawa kafin a tsaya takarar shugabancin siyasa, talaka ba zai iya ba, in ma sarauta ce masu neman kan kashe maqudan kudin da wasu 'yan siyasan ba sa kashewa, sannan su kansu masarautun sun ajiye shi a matsayin gado ne, komai cancantar mutum in ba a cikinsu yake ba to bai cancanta ba, shi ya sa banu Isra'ila suka ambaci wadannan abubuwan guda biyu, wato kusantaka da wadata, ba su damu da cancanta ba.
.
7) Manyan abubuwa guda biyu da suka dace a lura da su wurin dora shugaba su ne ilimi da lafiyar gabobin jiki gaba daya, duk al'ummar da ta dora mai laulayi a matsayin shugabanta ba abinda za ta iya tsinanawa, wannan ya sa aka gaya wa banu Isra'ila wadannan abubuwa guda biyu.
8) Akan nemi shugabanci, wani sa'in za ka ga al'umma sun zabi mutum guda wanda shi suke so, amma Allah SW ya ba da mulkin ga wanda ya so, wanda tunanin mutane a baya samsam bai taba kawowa kansa ba.
9) Bin dokokin da kwamandan yaqi ya gindaya abu ne da ya zama dole ga duk wata runduna matuqar tana son cin nasara a wannan yaqin da ta kutsa kai, ba wani abu ya karya banu Isra'ila ba sai qin bin umurnin shugabansu.
.
10) Duk wata runduna dake cin nasara a kan abokan gabanta da haquri, juriya da dagewa ta isa wannan matsayin.
11) Sai an hada da imani da Allah SW, da gasgata alqawarin da ya yi na ba da nasara a kan kafurci.
12) Komawa ga Allah SW a duk lokacin da aka shiga runtsu wurin yaqi abu ne mai mahimmancin gaske, Allah kan karbi buqatar mutane kuma ya ba su nasarar.
13) A tsarin rayuwa dole sai wasu sun canji wasu, wasu lokutan tsoron canjin ke sanya mutane su yi abubuwan da suka dace, a duk lokacin da mutum ya san cewa matsayin da ya taka dinnan ba mai iya cire shi sai ka ga yana yin abinda ya ga dama, tsige mutum ma wata falala ce garemu.
.
Haka sunnar Allah SW take a bayan qasa, duk lokacin da mutane suka qi bautar da aka kawo su a dalilinta sai a kawar da su a kawo wasu, zuwa lokacin da suka fara kawar da kawunansu a dalilin sakin layi, daga baya sai a sami wasu bayin Allan su dawo da al'umma kan hanya madaidaiciya, sai dai kuma an sami manzanni wadanda suke koyar da mutane saqon Allah SW, suke fassara musu abinda Allan yake nufi, yanzu sai ya zama babu manzanni, ga wata aya kuma ta sauko wace take cewa babu tilasta a addini, da wannan za mu ga babban abinda ya rage wa al'umma shi ne jahadi, wato aiki tuquru wajen ba wa kai da addini kariya bisa qa'idojin da muslunci ya tsara.
.
Duk manzanninnan da irin gwagwarmayar da suka sha ba inda haka kawai suka abka wa kafurai da duka da kisa, za ka taras da'awa suka riqa yi, sai lokacin banu Isra'ila ne suka fara kai farmaki don dawo da mabautarsu ko za su sami damar yin addininsu cikin kwanciyar hankali, jihadi bai nuna musu cewa su yaqi wasu don sun saba musu a fahimtar addini ba, mun ma ga yadda Musa AS ya yi ta fama da banu Isra'ila wasunsu ba ma musulmai ba ne amma ya kwashe su gaba daya, sai ya yi ta qoqarin shiryar da su, shugabanni kan yi qoqarin shiryarwa ne ba wai su rabu da mutum ta hanyar kisa ba.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248