JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 11
JALUTA DA BANU ISRA'ILA
Tun dauri kamar yadda muka sani Bukhtanasar ya riqa dandana wa banu Isra'ila kudarsu, da yawansu sun mutu a hannunsa, tunda ragamar tsarin rayuwarsu yanzu ba ta annabci ba ce, ta sarauta ce, ma'ana tsarin dan-adam ne zalla, ba shakka Allah SW ya yi musu falalar da bai yi wa kowa ba a cikin talikai don komai nasu daga Allah SW ne, kasancewar manzanni na raye a cikinsu, in mun lura mutanen dake gabaninsu in sun saba wa Allah SW halakar da su yake yi gaba daya, amma su ko sun sha wuya sai ka ga an turo wani annabin ya qwato su, akwai ma wani manzon da aka haife shi a cikinsu amma da Allah SW ya tashi tura shi sai ya aike shi Iraqi wato Nainawa, shi ne Yunus AS wanda suke kiransa da (Jonah).
.
Duk da wannan falala tasu ba su gode wa Allah SW ba, sai suka juyo kan annabawan suka riqa kashewa, Qur'ani ya yi maganar wannan aika-aikar tasu, don haka Allah SW ya rage turo musu annabawan ya bar su da shugabanninsu, a qarshe suka lallaba suka sami annabin wannan lokacin wato Sham'un AS (Schmuel) wasu suka ce Samau'il ne (Samuel) ya zabar musu wanda zai zama sarki duk su hadu a qarqashinsa su yaqi sarakunan dake ci musu tuwo a qwarya, ya gargade su da kar fa ya zabo musu din a zo yaqi ya wajaba musu su ce ba za su yi ba.
.
Suka ce da banza ma sun yi yaqin bare ga shi an kore su daga qasar da suke ganin tasu ce su da yaransu, {وَقَالَ لَهُمْ نَبِيُّهُمْ إِنَّ اللَّهَ قَدْ بَعَثَ لَكُمْ طَالُوتَ مَلِكًا قَالُوا أَنَّى يَكُونُ لَهُ الْمُلْكُ عَلَيْنَا وَنَحْنُ أَحَقُّ بِالْمُلْكِ مِنْهُ وَلَمْ يُؤْتَ سَعَةً مِنَ الْمَالِ قَالَ إِنَّ اللَّهَ اصْطَفَاهُ عَلَيْكُمْ وَزَادَهُ بَسْطَةً فِي الْعِلْمِ وَالْجِسْمِ وَاللَّهُ يُؤْتِي مُلْكَهُ مَنْ يَشَاءُ وَاللَّهُ وَاسِعٌ عَلِيمٌ} (Sai annabinsu ya ce: To Allah ya zaba muku Daluta ya zama muku sarki, suka ce ta ina zai zama mana sarki bayan mun fi shi cancanta sannan ba wata dukiya ce gare shi ba, ya ce: To Allah ya zabe shi a kanku ya ba shi yalwataccen ilimi ga jiki, Allah kan ba da mulkinsa ga wanda ya so, shi mai-yalwa ne masani).
.
Daganan suka nemi sai ya kawo musu wani abu da zai nuna cewa ya cancanta ya jagorance su, to kamar yadda muka sani ba ma qaryatawa ba har kashe annabawan suke yi, kuma dukansu sun tabbatar qwace akwatinsu na Musa AS da suke tabarraki da shi duk shi ya kawo su cikin wannan masifar, suna ganin da wahala su ci wani yaqi kuma, anan ne annabin nasu ya ce "To ai Daluta zai zo muku da akwatin don ya zama shedar cewa ya cancanci wannan matsayin" duka sai suka yarda, amma fa akwai wani sharadi wanda an gaya musu cewa jarabawa ce don tantance imaninsu da cewa sun shirya shiga yaqin.
.
Lokacin da Daluta ya jagoranci rundunar yaqin sai ya ce musu {إِنَّ اللَّهَ مُبْتَلِيكُمْ بِنَهَرٍ فَمَنْ شَرِبَ مِنْهُ فَلَيْسَ مِنِّي وَمَنْ لَمْ يَطْعَمْهُ فَإِنَّهُ مِنِّي إِلَّا مَنِ اغْتَرَفَ غُرْفَةً بِيَدِهِ فَشَرِبُوا مِنْهُ إِلَّا قَلِيلًا مِنْهُمْ} (Allah zai jarrabe su da wani kogi duk wanda ya kwankwade shi bai tare da mu wanda bai sha ba shi ke tare da mu, sai dai wanda ya dan kamface shi kamfata daya da hannunsa, ai kuwa suka kwankwada sai 'yan kadan daga cikinsu) wannan ya nuna ba su yi shirin shiga yaqin ba don wanda bai yi haqurin qishi na lokaci guda ba ta ya zai jure wahalhalun yaqi da matsalolinsa?
.
To wadanda suka narki ruwan sai suka jabe suka kasa shiga yaqin, kuma su ne ke da adadi mai yawa, sai 'yan kadan din da ba su sha ruwan sosai ba suka qara imani da jin qarfin shiga yaqin, haka rundunar ta yi gaba, a wannan lokacin Annabi Dauda AS (wanda suke ce masa David) yana matashi, kuma an yi dace yana cikin rundunar, cikin ikon Allah sai suka sami nasara Dauda AS ya sami sa'ar kashe Jaluta, wannan kisa ta fitar da shi don ba qaramin qoqari ya yi musu ba, shi ya sa ma aka tsayar da shi a matsayin sarki kafin daga baya Allah SW ya aiko shi a matsayin manzo, a wannan lokacin jagoranci ya dawo hannun muslunci.
.
DAUD AS
Asali kamar yadda tarihi ya muna shi matashi ne mai danyen jini, sana'arsa kiwon tumaki ne ba wanda ya san shi a tsakanin masu ruwa da tsaki na banu Isra'ila, sai dai Allah SW ya azurta shi da kashe Jaluta, masu tarihi sun fadi jarumtarsa ba wai don ya shiga yaqin ba, yadda ya iya fuskantar Jalutan har Allah SW ya ba shi sa'ar kashe shi, wannan namijin qoqari banu Isra'ila suka gani har suka iya nada shi a matsayin sarkinsu ba tare da kallon danganensa ko halinsa na kudi ba kamar yadda suka yi yayin nada Jaluta, sai dai da yawa cikin banu Isra'ila har yanzu suna daukar Daud AS a matsayin sarki ne kuma bawan Allah ba annabi ba kamar yadda yake a Kiristanci da Muslunci ba.
.
Muslunci ya tsayu sosai a zamanin Daud AS, duk da haka sun saki hanya dalilin aiko musu manzo,
kenan wato Dauda AS, Allah SW ya ce { لُعِنَ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ بَنِي إِسْرَائِيلَ عَلَى لِسَانِ دَاوُودَ وَعِيسَى ابْنِ مَرْيَمَ ذَلِكَ بِمَا عَصَوْا وَكَانُوا يَعْتَدُونَ} (An la'anci wadanda suka kafurta cikin banu Isra'ila ta harshen Dauda da Isa dan Maryam saboda sabawarsu da wuce gona da iri) Ma'ida78. Allah ya hore wa Annabi Dauda AS duwatsu sukan yi tasbihi tare, kamar yadda ya hore masa qarfe yakan iya yi masa karyar alawa, ga hikima wurin yanke hukunci, hadisi ya koyar da mu yadda yake ibadarsa masammam azumi, duk da haka bai tsira ba a hannun banu Isra'ila, muslunci dai ya dawo da qarfinsa shi yake jagoranci.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248