( MIJI NAGARI 02. )
5th/muharram/1443.AH-14th/august/2021_
11. Miji nagari shine wanda yake ciyar da iyalinsa idan shima yaci, yake shayar dasu idan shima yasha. Kuma yake tufatar dasu idan shima ya tufatar da kansa.
12. Miji nagari shine wanda ya É—auki aure amatsayin Ibadah, ba wai sha'awa ko kuma abin wasa ba.
13. Miji nagari shine wanda ya ɗauki matarsa amatsayin abokiyar rayuwar sa kuma abokiyarsa, ƙanwarsa, ɗalibarsa, kuma abokiyar shawararsa.
14. Miji nagari shine wanda ba ya zagin matarsa, baya cin mutuncinta, ba ya cin zalinta, kuma baya ha'intarta.
15. Miji nagari shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa da farin ciki koda kuwa basuda wadatar arziki.
16. Miji nagari shine wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake haƙurin zama da ita tare da kyautatawa akowana irin yanayi.
17. Miji nagari shine wanda idan zai yi magana da matarsa, zai faɗi gaskiya babu yaudara ko ƙarya, bare kuma cin amana acikin ayyukansa da kuma zantukansa.
18. Miji nagari shine wanda ya É—auka azuciyarsa cewar: Iyayen matarsa, Iyayensa ne. Æ´an uwanta ma Æ´an uwansa ne. Danginta ma danginsa ne.
19. Miji nagari shine wanda yake É—aukar farincikin matarsa shine farincikinsa. Kuma damuwar ta, shima damuwar sace.
20. Miji nagari shine yake ƙokƙrin kiyaye sirrin matarsa, kuma yake ƙoƙarin Kare mata mutuncinta koda awajen ƴan uwansa ne, tare da hikima da fahimtarwa.
21. Miji nagari shine wanda baya fifita matarsa akan ƴan uwansa, kuma baya tauye mata haƙƙinta da kuma tauye darajarta. Yana ba ma kowanne ɓangare nasa haƙƙin.
22. Miji nagari shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da haƙuri acikin zuciyarsa domin ya riƙa kashe wutar tashin hankali da ɓacin ran matarsa, aduk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa.
23. Miji nagari shine wanda akullum yake ƙoƙarin tarbiyyantar da iyalinsa abisa rayuwa irinta addinin Islama ba rayuwa irinta turawan yamma da maguzawa ba.
24. Miji nagari shine wanda yake zaune da matansa komai daÉ—i komai wuya ba zai dena nuna masu soyayya ba.
25. Miji nagari shine wanda yake kallon matar sa amatsayin sarauniya Komae talaucin iyayen ta da yalwar arzikin sa.
Muna roqon dhul arshil majeedu fa'aalun limaa yureed, da ya haÉ—a matayen mu da mazaje nagari, muma kuma ya haÉ—amu da mataye nagari, alfarmar ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD IBN ABDALLAH, (S.A.W)
Zamuci gaba Inshaa Allaah.
Daga ÆŠan uwanku a Musulunci.
(Ustadh_Abulfawzhaan)