MUGUN ABOKI - ƘARSHE



*MUGUN ABOKI...................*

👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬

             *FUTOWA TA 👇*
                  *QARSHE*

  
*MU'AMALA DA ABOKIN BANZA*
    
    Gareka mai karatu munyi magana dan gane da aboki na banza da Siffofinsa da cutarwar da yake da ita, amma akwai yana yi da dole sai kayi Mu'amala dashi kuma kaima zaka iya kata rawa wajan gyara masa dabi'u da halaye ta hanyar nasiha da nusantarwa, sai dai a irin wannan halin dole sai ka kare kan ka daga gareshi da kuma sharrinsa abubuwan sune kamar haka :

*1- IYA KANCE MU'AMALA TARE DASHI* idan ya kasance cikin abokanka akwai wanda ba nagari ba yana aikata miyagun dabi'u wadanda basu dace da dabi'u irin naka ba, Abu na farko da zaka fara yi shine ka iya kance mu'amalarka dashi da takofi mai kaifin gaske, ya kasance haduwarka dashi sai a irin gurin da babu makawa, kada ka dunga basa damar haduwa da kai, ba laifi bane idan ka gaya masa cewa yanzu alaqarka dashi baza ta yuwu ba kamar abaya saboda abun da ka saka agaba yanzu bai bari ku cigaba da alaqa dashi ba, bayan cewa kai kasan cewa saboda miyagun dabi'unsa ne yasa ka nisan ceshi. 

*2- KA KARE KAN KA SOSAI* kare kai yana daga cikin al'amura masu mahimmanci wanda ya kamata ka kula dashi ya yin alaqa da aboki na banza, dole ne ka kiyaye sirrinka ya kasance nesa garesa, ka nisanci shiga tare dashi cikin iyalanka ko al'ummarka, zai fi kyau aboki na banza ya zama nesa ga gidanka da kuma danginka, kuma ya yi nesa da duk abun da ya shafi sunanka. 

*3- YANKE ALAQA* yanke alaqa da abokin da kuka taso tare dashi bayan ya bayyana gareka cewa mutumin banza ne abune mai wahala kuma mai tattare da matsaloli amma dole hakan zakayi domin shine mafuta gareka. 

*4- NASIHA* idan ya kasance abokinka miyagun dabi'u da halaye da yake dauke dasu asali ba haka dabi'u,da halaye,da tarbiyyarsa suke ba, yana da kyau ka dunga yi masa nasiha tare da nusantar dashi, akan miyagun dabi'un da ya dauka , sai dai kada ka kai maqura wajan yi masa, idan bai amsa maka ba akan wannan nasihar da kake masa , abu mafi kyawu gareka, ka tafi kabarsa kayi nesa dashi. 

*5- KA TSAWATU DAGA ABOKI NA BANZA* A wani yana yin babu ta yadda zaka iya yanke alaqarka da aboki na banza kai tsaye, ta iya yuwuwa makocinka ne makusanci, ko kuma abokinka na yarinta, wani lokacinma zai iya kasancewa daga cikin danginka, wanda babu ta yadda za'ayi kayi rayuwarka ba tare da shi ba, to a irin wannan halin ka kasance a fadake da tafiya a bayansa cikin al'amura domin kubutar da rayuwarka.


*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibai masu neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
       *(UMMU HANAN)*
       🥏08026799975🥏

Post a Comment (0)