MUGUN ABOKI 10

*MUGUN ABOKI...................*

👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬👬

             *FUTOWA TA 👇*
                    *(10)*


*CUTARWAR ABOKIN BANZA DA TASIRINTA GA ABOKINSA*

     Daga cikin cutarwar abokin banza ga abokinsa sune kamar haka :

*1- NASON SHARRI DA FASADI* abota da aboki na banza zai saka ka zama mabarnaci kamarsa, domin shi aboki na banza yana qoqari ne ako da yaushe ka zama irinsa, ko da ace kai mutumin kirki ne kana so abokinka ya zama nagari kamar yadda kake nason miyagun dabi'unsa yafi yadda yake nason kyawawan dabi'unka don haka hanya mafi kyawu ka nisanci mu'amala da shi. 

*2- KOYAN MIYAGUN DABI'U* babu makawa idan ka lazimci zama da abokin banza sai ya koya maka miyagun dabi'u, kuma zai yi iya bakin kokarinsa sosai wajan koya maka, domin baya san ya kasance shi kadaine mai aikata hakan, kasani ya kai mai karatu abokin banza yana qin ace ka fisa wajan kyawawan dabi'u, da kyakykyawar shaida wajan mutane, don haka yi qoqari wajan nisantar da kan ka daga garesa. 

*3- MUGUWAR SHAIDA A GURIN MUTANE* ba wai kawai akan dabi'unka Al'umma suke gina hukuncinsu akan ka ba, a a suna hadawa da dabi'un abokanka, idan al'umma suka san cewa kai abokin wane ne to sun san ya ya dabi'unka suke, domin abokin aboki nagari shima nagarine a wajan mutane, haka zalika abokin aboki na banza shima na banza ne a wajan mutane. 

*4- SAKA KA CIKIN MATSALOLI* Bazai taba yuwu wa ba ka lazimci zama da abokin banza ba tare da ka afka cikin matsaloli ba, domin zaka iya samun kan ka cikin tuhuma ta sata kwatsam ba tare da kasani ba, ma'abota haqqi zasu kwankwasa maka kofa alhali ba kai kayi musu sata ba, sai dai abokin ka ne!. cikin da yawa daga cikin al'amura aboki na banza zai yau dare ka har ya jefa ka cikin abun da ba halinka ba. 

*5- CUTARWA TA KAI TSAYE* Aboki na banza zai cutar da kai cutarwa ta zahiri, wadda zata kai ka zuwa ga koyan sata da sauran miyagun dabi'u har ta kai wannan cutarwa ta kai zuwa ga cikin iyalanka, babu yadda za'ayi ka kubatar daga irin wannan cutar face ka nisance shi.


*UBANGIJI KA NISANTAR DAMU DAGA MIYAGUN ABOKAI*


*MU HADU A FUTOWA TA 11*

*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibai masu neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
*MARYAM HUSAIN ABDULLAH*
       *(UMMU HANAN)*
       🥏08026799975🥏

Post a Comment (0)