ANSAMU HIKIMA AWURIN WANDA AKA DAUKA MAHAUKACI NE

ANSAMU HIKIMA AWURIN WANDA AKA DAUKA MAHAUKACI NE.


Wata rana bayan rigima ta barke mai kaushi tsakanin wasu ma'aurata, sai mijin yayi rantsuwar saki ga matarsa yace mata, bazaki dawo cikin kulawata ba sai rana mai shu'umci Mara alheri, mara haske. Matan tatafi gidan iyayenta.

Bayan yasamu nutsuwa, sai yayi nadama akan hakan yakuma fita Neman fatawa akan wannan matsala acikin garinsu, bayan yahadu da malamin garinsu yamasa bayani.
Sai malamin yace bakada mafita ina zan samoma rana shu'uma hargitsatstsiya Mara haske? Saidai katafi acikin birni kasamu malamin daya fini kila yasama maka mafita.

Sai mijin yadawo gida yayi shirin zuwa birne tunda sassafen gobe,yayi gaggawan fita zuwa birni yaje babbar jami'a yayi sallar azahar don yasamu yatambayi limamin gameda rantsuwan saki dayayi, saidai amsar shi irin amsar nafarko ne, daga ina zanzoma da irin wannan rana?

Sai yatafi kasuwar garin yana cikeda bakinciki da damuwa na rashin sanin mafita ya zauna shuru batareda kula kowa ko sauraren kowa ba, yayin da wani mai saida kaya yalura da halin dayake ciki dai yatambaye shi, menene damuwarka bawan Allah? Lokacin daya bashi labari, sai yace duba damanka gawani mutum can kaje katambayeshi gameda matsalarka.

Lokacin daya juya yakalli mutum in ga mamakinsa yana a hargitse azaune akasa dirshan, gashin kansa acukurkude. Yace wancan? Yace eh, sai yatafi acikin sanyin gwuywa aransa yana cewa malamai ma sun rasa min mafita bare wannan!!

Sai yace masa ya bawan Allah inaso inbaka labarina, yace ina saurarenka. Sai yabashi labarinsa har karshe.

Sai yace masa yau kayi sallar asubah? Yace ina arude wallahi banyiba.
Yace Yaya mahaifiyarka take yau? Yace bansamu ganinta yau ba ina gaggawa infita neman mafita tun sassafe.
Sai yakara cemasa, me kakaranta na alqur'ani yau? Yace acikin fushi nace maka yau hankalina atashe yake kuma ban ziyarci kowa ba.

Yace masa jeka kadawo da matarka, shin ina zaka samo wata rana datafi wannan shu'umci, hargitsatstsiyar rana Mara haske? Ranar da bakayi sallar asuba ba, baka karanta Qur'an ba kuma baka gaisarda mahaifiyarka ba

Sai yayi farinciki ya sumbaci kan Wanda yayi tunani mahaukaci ne, yace kaceto ni ya malam kuma mai sani.
Yace mekake so inbaka? Sai yace bana Neman komai sai awurin ubangiji mahaliccina.

DARASI..............
Ka'iya ganin abinda kake nema a'inda bakayi tsammani ba.
Ilimi acikin kiraza yake, ba'a sanya tufafi masu daraja da nuna girma ba.
Kashedinka kada karaina kowa.

Ya Allah kasanya mahaifiyata data sauran musulmi a madaukakin matsayi acikin aljanna.
.
Post a Comment (0)