FALALAR GOMAN FARKO NA ZULHIJJA.

FALALAR GOMAN FARKO NA ZULHIJJA.


1) Allah yayi rantsuwa dasu a cikin alQurani. Qur'an 89:2.

2) Sune Ayyamun Ma'alumat da Allah ya umurci ayi ambaton sa a ciki a suratul Hajj Qur'an 22: 28.

3) Aiki a cikin su yafi falala da lada da soyuwa ga Allah akan duk sauran kwanakin shekara. Bukhari no.926.

4) Anaso a yawaita Subhanallah, Walhamdulilllah, wallahu Akbar wa Lailaha illallah da karatun al-Qurani. Bukhari ya ruwaito.

5) Anaso a bayyana ambaton Allah aciki domin a tunawa wanda yamanta. Abdullahi Ibn Umar da Abu-Hurairah sun kasance suna shiga kasuwa suna kabbara jamaa na kabbara da kabbarar su. Bukhari ya ruwaito .

6) Aikin Hajji yana cikin Ayukka mafi falala a cikin wadanna kwanaki.

7) Annabi S.A.W yakasan ce yana azumin kwanaki tara na farkon Zulhijja. Ahmad da Abu-Dawud da Nasai suka ruwaito . Albani ya inganta a Sahihi Sunani Abi-Dawud 2106.

8) Azumin Ranar Arafah yana karkare zunubban shekarar da ta wuce da wadda zata zo . Muslim 1162.

9) Idan kwanakin goma suka shigo wanda keda niyyar layya bazai cire gashi ko kumba a jikin sa ba. Muslim ya ruwaito.

10) Hadisin da ake ya wo dashi na Allah ya karbi tuban Annabawa a cikin kwanaki goma na Zulhijja, bai inganta ba kuma baya Halatta a watsa shi kamar yadda Sheikh Abdurrahman al-Suhaimi yayi bayani.

✍️
Dr. Jabir Sani Maihula.
.
.
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*

1 Comments

Post a Comment