MUN SHIGA WATAN DHUL HIJJAH

MUN SHIGA WATAN DHUL HIJJAH


💧 Mun shiga watan Zhul hijja, kada ku yi sakaci a cikin kwanaki goman farkon nan, ta yiwu wasu alkhairi masu yawa sun wuce ka a Ramadhan to ga dama ta samu, kwana goma ne ba yawa, se dai ayyuka alkhairi suna da girma wurin Allah. 

🌹An karbo daga Abdullahi ɗan Abbas Allah ya yarda dashi yana cewa Manzon Allah yace "Babu wani aiki wanda yafi tsarkaka a wajen Allah sannan kuma yake da girman lada fiye da aikin da aka yishi acikin kwanakin goman layya" sai akace masa harda jihadi? sai yace eh! harda jihadi sai dai wanda ya fita da dukiyarsa,sannan babu wanda ya dawo acikinsu"سنن الدارمي ٢/١٧٧٤

💧Mu dage da ayyuka alkhairi kada mu yi sakaci da damar mu, Mu yawaita karanta Al_K'ur'ani da sauran nau'ikan Zikiri, Azumi, Sadaka, tausaya masu rauni, Nafiloli (Sallan dare) sada zumunta da dukiya, da kuma ziyara, watsa alkhairi da ilmi tsakanin mutane da yawaita kabbarori. 

Allah Ta'ala yasa mu dace.

#Zaurenfisabilillah 

TELEGRAM:
 https://t.me/Fisabilillaaah
Post a Comment (0)