BUDURCI! BUDURCI!! BUDURCI!!!
Tabbass Budurci shi ne 'kimar mace, kuma shi ne babban girman mace, sannan babu daraja da mutuntawar da mace za ta yi wa mijinta kamar a ce ya sameta a budurwa lokacin da ya aureta.
Mutuncin Budurci ya samo asali ne tun tale-tale, inda ake samun 'kabilu da su ke girmama sha'aninsa, har idan aka yi aure to sai an shimfid'a farin 'kyalle a zo washe gari dubiyar jini, idan ba a gani ba to akwai ayar tambaya akan amaryar, idan kuwa an gani to bushara da d'aukaka sai wanda ta gani.
SHIN BUDURCI HAR YANZU YANA DA 'KIMA?
Wani zai yi mamakin wannan tambayar.
Dalilin yin wannan tambayar shi ne : sau da yawa za ka dinga ganin wasu da su ke ikirarin wayewa su na cewa, budurci ba shi ne 'kima ba.
Lokacin da ina Service, a CDS d'ina ina group d'in Sdgs ne, to an ta'ba gayyatar wani likita ya zo ya yi mana lacca akan FGM wato "Female Genital Mutilation"
Wato Yankan gishiri ko yi wa mata kaciya, to a nan wannan likita ya kad'a baki yace :"Virginity is nothing" wato budurci ba komai ba ne, lokacin da yake batu akan cewa daga cikin illolin yankan gishiri akwai tafiyar da budurci.
To wannan maganar tana da fuska biyu :
1-Shi kansa budurcin (Virginity) .
2-Tantanin budurci (Hymen) .
In har na farkon ne wato tafiyar budurci ta hanyar aikata Zina to wannan sam-sam ba sai mun yi maganar 'batancinshi ba.
Batun tantanin budurci : tantanin budurci wata fata ce shara-shara da ke al'aurar mace, tana nuni akan cewa wannan mace budurwa ce babu abun da ya ta'ba shiganta.
Amma shin tantanin budurci shi ne yake nuna cewa mace budurwa ce? Rashin shi kuma yana nuna mutuniyar banza ce? Idan mutum ya auri mace ya tarar da ba ta da wannan tantanin shin ya zai yi?
Ga amsar da Sheikh Bin Baaz ya bayar :
HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE YANA TSAMMANIN BUDURWA CE SAI YA BAYYANA MASA CEWA BA BUDURWAR BACE :
"Mai tambaya : idan Mutum ya auri Mace akan cewa Budurwa ce, bayan ya ke'be da ita sai ya tarar da ita ba a matsayin budurwa ba, to ya zai yi?
Ash-Sheikh Abdul-Azeez Bin Baaz R.A Ya ba da amsa akan wannan tambaya yace :
"hakan yana da dalilai, ta yuwu budurcin ya tafi ba ta dalilin aikata Zina ba, dan haka ya wajaba a kyautata mata zato matu'kar a zahiri mutuniyar kirki ce, kuma a zahiri tsayayya ce a addini, dole a kyautata mata zato saboda hakan, ko kuma ta ta'ba aikata alfasha amma ta tuba kuma ta yi nadama daga baya alheri ya bayyana gareta, to hakan bazai cutar da shi Mijin na ta ba, kuma ta yuwu budurcin na ta ya gushe ne saboda tsananin jinin Al'ada da take yi, domin lallai tsananin jinin Al'ada yana gusar da budurci kamar yadda Malamai su ka ambata, Wani lokaci kuma budurci yana gushewa ta dalilin tsalle tsalle daga wani waje zuwa wani wajen, Ko ta sauko daga saman wani waje zuwa 'kasa da 'karfi, budurci ya kan gushe ta dalilin hakan, ba lallai bane sai ta hanyar aikata zina yake gushewa ba, a'a, idan Mace ta yi ikirarin gushewar budurcinta ta wani dalilin da ba alfasha ba to babu matsala, ko kuma ta hanyar alfasha ne amma sai dai ta ambata cewa tilasta ta akayi ko fyad'e aka yi mata , wannan ma bazai cutar da shi ba, idan har ta yi jini d'aya bayan faruwar lamarin (domin istibra'i), ko ta ambaci cewa ta tuba ta yi nadama, kuma ta aikata hakan ne da rashin sani bisa kuskure sannan ta tuba ta yi da na sani, hakan bazai cutar da shi ba, kuma bai kamata ya yad'a hakan ba, kuma ya kamata ya rufa mata asiri, idan ya tabbatar da cewa tana da gaskiya kuma tsayayya ce kan addini, to ya zauna da ita ko ya saketa tare da rufa mata asiri Kada ya bayyana abun da zai kawo sharri da fitina"
Majmu'u fatawabni Baaz (20/286).
To kenan budurcin mace ya kan kau ba dole sai ta dalilin aikata alfasha ba.
To shin budurci ko Tantaninshi yana da 'kima a musulunce? Idan wani ya kawarwa da wata akwai tanadajjen hukunci?
Ya zo a cikin littafin Ash-Sharhul Mumti'u :
وأرش البكارة هو : فرق ما بين مهرها ثيِّباً ، ومهرها بكراً ، فإذا قلنا : إن مهرها ثيِّباً ألف ريال ، ومهرها بكراً ألفان : فيكون الأرش ألف ريال " انتهى .
" الشرح الممتع " ( 12 / 313 ، 314 ) .
والله أعلم
Wato : Hukuncin da za a 'kaddara na tantanin budurci shi ne : bambanci tsakanin Sadakinta idan tana bazawara, da sadakinta idan tana Budurwa, idan mu ka ce : Sadakinta idan tana bazawara shi ne 1000,idan tana budurwa kuma 2000, to kud'in da za a ba ta in an tafiyar mata da budurci (bisa zalunci) shi ne 1000.
Amma a wajen abu Haneefa : bayan ya biya wannan, dole kuma sai ya biya Sadakinta.
Al-ma'anil Badee'ah (2/43)
A cikin littafin Minhaajud-'Dalibeen kuma ya ce akwai sa'bani akai amma abun da ya fi inganci shi ne za a biya diyya ne daga jinsin ra'kuma kamar yadda ake biyan diyyar ga'bo'bin jiki.
Amma wannan idan an gusar ne ba ta hanyar Jima'i ba, kamar da yatsa ko icce, amma idan ta hanyar saduwa ne to shi ne za a biya Sadakin kwatankwacinta a cikin matan garinsu.
Idan kuma mijinta ne ya gusar in ta hanyar saduwa ne babu matsala, amma idan wata hanya ya bi to an yi sa'bani, amma mafi inganci, babu komai a kanshi.
Minhajud-'Dalibeen (7/161).
To dan haka kada wani ya zugaki cewa budurci ba komai ba ne, a'a har yanzu yana da 'kima sosai kuma har gobe, wad'ancan maganganu da ake fad'a idan an samu matsala ne.
Akwai artificial hymen da ake yi a wannan lokacin, bayan mace ya gushe mata sai ta ce bari ta je ta yi sabo a d'inketa a matseta don kada angonta ya gane ba budurwa ba ce.
To ki sani in har kin 'boye masa ba za ki 'boyewa Allah ba.
Malamai sun yi magana akan idan miji ya shard'anta cewa budurwa ce kuma ya same ta ba haka ba, sun yi sa'bani wasu suna ganin yana da ikon warware auren, amma ba shi da sadaki matu'kar ya kusanceta.
Wallahu A'alam.
Allah Ya kiyayemu Ya kiyaye mana zurriyar mu.