HUKUNCIN YIN JAM'I GUDA BIYU A MASALLACI GUDA DAYA!
Tambaya
Assalamu alaikum malam, halaccin sabunta wani jam'i a masallaci bayan angama nafarko
Amsa
Wa alaikum assalam, ya halatta a sabunta, hakan kuma Mustahabbi ne.
Annabi (SAW) ya ga wani ya zo bayan an yi Sallah, sai ya ce "Wa zai yiwa wannan Sadaka, ya yi Sallah tare da shi?" kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi mai lamba ta (220).
Babu hadisi bayyananne yankakke wanda ya hana maimaita jam'in Sallah a Masallaci.
Annabi (SAW) yana cewa:
"Sallar Jam'i ta fi sallar mutum daya da daraja (27)", duk nassin da yake gamamme ana barin shi a yadda yake sai in an samu dalilin da ya cire wani abu a cikin shi ko ya rage masa karfi .
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
04-03-2020
Miftahul ilmi
Facebook ⇨https://www.facebook.com/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM ⇨https://t.me/miftahulilmii
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248