ZAN IYA ZUBAR DA CIKIN DA NA TABBATAR SIKILA NE?
Tambaya:
Slm mallam ni AS ce, mijinama ma desame genotype muke da shi, yarana biyu babban AA karamar AS, duk sanda na sami chiki muna zuwa a duba mana genotype din babyn dake chikin, likitochi suka tabbatar da SS ne sai musa a chire, amma bai kaiwa 4months muke chirewa, mallam meye hukunchin yin hakan ?
Amsa:
Wa'alaikumus salaam wa rahmatullahi wa barakaatuhu, To 'yar'uwa Malamai sun yi ijma'i akan haramcin zubar da ciki bayan an busa masa rai, saboda ya zama kashe rai ba da hakki ba.
Amma sun yi sabani game da zubar da ciki kafin ya kai watanni hudu, wasu sun haramta, wasu kuma sun halatta wasu sun karhanta
Amma abin da yake daidai shi ne ya halatta a zubar da cikin da bai kai wata hudu ba, idan akwai lalura, zubar da cikin Scler ba dole ya zama lalura ba, tun da ana iya haihuwarsa ya rayu, ya bautawa Allah ya amfani al'uma, don haka barin cikin shi ne ya fi, saidai idan kuka zubar kafin ya cika wata hudu saboda matsalar da kuke tunanin yaron zai iya fuskanta a rayuwarsa, ba za'a ce kun yi laifi ba, tun da bai zama mutum ba, kuma ba za'a tashe shi ranar alkiyama ba.
Don neman karin bayani duba Ahkamu al-janin fil-fiqhil islamy na Umar Ganam.
Allah ne mafi sani.
18/10/2015
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.