JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 13

JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 13
.


ME ZA MU KOYA A CIKI?
Allah SW bai ba Annabi SAW qissar magabata don kawai ya ji yadda suka qare ba, kwantar masa da hankali aka riqa yi don ya san cewa magabatansa ma fa sun kwankwandi irin wadannan matsalolin amma suka haqura, sannan akwai wasu darussa na masamman da ake son ya dauka a ciki, mu dauki qissoshin banu Isra'ilannan a matsayin misali:-
1) Yawan mabiya da rundunar yaqi ko tarin makamai kar su taba yaudarar shugabanni, su bincika qarfin mayaqan tukun, da irin qarfin imaninsu wurin fuskantar duk wani yaqi da za shiga.
.
Ba domin jarabawar da Daluta ya yi wa sojojinsa ba da ya zaci cewa duk yawannan a shirye suke su yi qundumbala cikin duk yaqin da za a kutsa ko a mutu ko a yi rai, amma da ya yi musu jarabawa sai ya bayyana masa 'yan qalilan ne kawai suke da shirin shiga yaqin bil-haqqi da gaskiya.
2) Haka jarabawar da za a yi wa mutanen kar a taqaita ga ta farko kawai, ko a wannan qissar akwai misali:-
a) Banu Isra'ila ne suka nemi a yi yaqin, ana wajabta musu suka kau da kai sai 'yan qalilan daga cikinsu wato wadanda suka raka Daluta.
.
b) A lokacin jarabawar farko duk suka zube, suka sha ruwan da aka yi musu kashedin shansa, 'yan qalilan ne matuqa suka ci jarabawar.
c) Su ma wadannan kadan din ba su iya jurewa zuwa qarshe ba, lokacin da wuta ta yi wuta sun yi rauni a gaban dubban abokan gaba.
d) Har wayau wadannan din suka sake ja da baya sai wasu 'yan qalilan daga cikinsu wadanda suka iya tsayawa su fuskanci abokan gaba, su ne wadanda Allah SW ya ba su nasara suka iya cin yaqin, kenan jarabawar farko ba ta sa wadanda suka yi nasara sun kawo abinda ake buqata ba, da Hausa ma akan ce ba a yabon dan kuturu sai ya mutu da yatsu.
.
3) A wannan yaqin duk wasu alamu da za su nuna cancantar Daluta da shuganci sun bayyana, su da suke cewa sun fi shi usuli da dukiya gashi duk sun arce, alamomin da za a yi la'akari da su sun hada da:-
a) Saninsa da cewa zai yuwu wasu su gudu akwai buqatar jarabawa.
b) Bai yaudaru da yawan mabiya kamar yadda wasu shugabannin bangarorin addini suke yi a yau ba.
c) Gwadawar farko ba ta gamsar da shi ba, kenan akwai buqatar daukar wasu hanyoyi na kariya.
d) Qoqarin gwada biyayyarsu ya gani ko suna da qarfin niyya da gaske.
e) Ware wadanda suka fadi jarabawan da cewa ba za a fita sahu guda da su ba.
.
g) Gashi dai mafi yawan mayaqan sun fadi jarabawa sai 'yan kadan, amma wannan bai karya masa qarfin gwiwa ba ya ji cewa ba za su iya ba, ya kwashi kadan din ya shiga yaqin da su hakannan.
h) Zuciyar dake tare da Allah koyaushe nasara take kallo sama da asarar da ake tsammanin tana gaba, wani rauni bai tasowa don aikin Allah za a yi kuma shi ne mai ba da qarfin, shi ke ba da nasarar, a qarshe rundunar Daluta ita keda nasara tare da rashin qarfinta ko rashin yawanta, za mu zo wannan a gaba a tarihin fiyayyen halitta, faruwar da'awarsa da korarsa daga Makka, da yadda Makkawan suka yi ta kai masa farmaki a waje, amma daga bisani aka bude qasar ba tare da yaqi ba.
.
Zuciya kan gaya wa mutum cewa ya isa, ko shi kadai zai iya yin abu, banu Isra'ila sun raina danganen daluta da arziqinsa amma shi ya jagorance su a qarshe, saboda ya zo musu da akwatin da suka tabbatar sun yi asararsa, a lokacin jarabawa kuma sun fadi don sun sha ruwan da aka ce kar su sha, a wurin yaqi kuma sai ga qaramin yaro makiyayi wato Dauda AS ya kashe musu babban wanda yake damunsu, anan akwai wani abin koyi, qwazon mutum ke nuna cancantarsa a wurin shugabanci, shiga fagen fama shi yake nuna cewa zai iya ko ba zai iya ba, Dauda AS da Daluta sun nuna bajintarsu da cancantarsu (Ma'a qisasis sabiqin fil Qur'an 1/332)
.
Wannan nasara da banu Isara'i suka samu ba ta zo musu a cikin sauqi ba, sun saba wa Allah 'yar falalar da suke samu kab suka rasa ta, suka qi bautar Allan aka kore su daga qasar da suke ganin sun samu, suka koma kashe annabawansu Allah SW ya komar da lamarinsu suwa hannun sarakunansu yadda suka yi ta gasa musu gyada a hannu, sai su da kansu suka gano sun saki hanya suka nemo mafita wurin annabinsu na wannan lokacin, ba su yi tunanin su dauki makami su fara karkashe mabarnatansu ba, ba su kafurta juna ko tunanin cewa aiki da qarfi zai yi maganin matsalar ba.
.
Mu a yau ba Annabi SAW a tsakaninmu Allah SW ya yi masa wafati shekaru da dama, amma fa ya bar mana littafin Allah wanda za mu riqa karantawa muna jin shiriyarsa, kamar dai wahayin da muke buqata kenan a kowani lokaci, in kuma mun buqaci ganin Annabinmu don tambayarsa wasu abubuwa da suka shiga mana duhu a rayuwa to ga hadisansanan, karanta hadisi da aiki da shi shi ke kawo zama lafiya ga musulmi, kuma al'ummannan ba za ta taba tabewa ba matuqar Annabi SAW na cikinta ko tana aiki da maganganunsa" (Gumi, Hasken muslunci FRCN) Mu a yau mun rage nemo masu shiga addinin mun koma korar wadanda suke cewa su musulman ne, ga aibanta manyan malamai.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
MIFTAHUL ILMI

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)