NASIHA GAME DA SALLAH.
.
Bismillahir Rahmānir Rāheem.
Gabatarwa:
Godiya ta tabbata ga Allah Maďaukakin Sarki, muna gode masa, muna neman taimakonSa kuma muna neman gafararSa, kuma muna neman tsarinSa daga sharrance-sharrancen kawukanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai iya 6atar da shi, kuma wanda Ya 6atar babu mai iya shiryar da shi. Ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (ﷺ) bawanSa ne kuma manzonSa ne.
Bayan haka 'yan uwa, ina yi maku gaisuwa irin ta addinin Musulunci; Assalāmu alaikum Warahmatullah Wabarakatuh.
.
'Yan uwa masu girma! Haqiqa Sallah ibadah ce mai girman gaske, kuma ita ce rukuni na biyu daga cikin rukunnai guda biyar da aka gina Musulunci da su kamar yadda ya tabbata a hadithi. Don haka ne Annabi Muhammad (ﷺ) ya ce ku umarci yaranku da yin sallah tun suna shekara bakwai (7), kuma a buge su idan sun kai shekara goma (ba su sallah). Idan har za a umarci a bugi yaron da be balaga ba idan ba ya sallah, to ina ga kuma wanda ya isa misali?!
Sallah ibada ce da ke kara kusanci tsakanin bawa da UbangijinSa, ibadah ce da ke haskaka rayuwar mai yin ta, kuma tsayar da sallah yana nisanta mutum daga alfasha da abin qi.
Haqiqa Allah Ya yi tanadin azaba mai tsanani ga wanda ya kasance yana tozarta sallah, kamar yadda Ya faďi:
”فَوَيلٌ لِّلمُصَلِّينَ. الَّذِينَ هُم عَن صَلَاتِهِم سَاهُونَ“.
Ma'ana: “To, bone (kwararon azaba) ya tabbata ga masallata. Waďanda suke masu shagala daga sallarsu”. (Suratul Mā'oon: 4-5). Wannan fa azabar ba ta marasa yin sallah bace, A'a, ta masu yin sallah ne amma waďanda suka shagala suke tozarta sallah, yana daga cikin tozarta sallah; qin yin sallah a kan lokacinta, rashin inganta tsarkin jiki da na tufafi, shagaltuwa da ababen duniya lokacin sallah, yin sallah sa6anin yadda Annabi (ﷺ) ya koyar, d.s.
Barin sallaah na nufin mutum ya yi watsi da sallaah, yana da lafiya da damar yin Sallaah Amman sai ya ki yi. Game da wannan, yawancin Malamai na ganin cewa duk Wanda ya bar sallaah tofa lallai ya bar musulunci, domin manzon Allaah (SAW) ya ce Sallaah ita ta bambanta mu da kafirai.
Kuma Hakika akwai horo mai tsanani a wajen Ubangiji ga wanda ya bar Sallaah.
Allaah madaukakin sarki Ya ce:
”ما سلككم في سقر{٤٢}
“Meya shigar da ku a cikin (wutar) saqar?"
”قالو لم نك من المصلين {٤٣}“
“Suka ce: ba mu kasance cikin masu Sallaah ba."
Sannan Manzon Allaah tsira da amincin Allaah sukara tabbata a gareshi ya ce : “Bambancin kasancewa musulmi da kasancewa kafiri shine Barin sallaah." (Muslim).
.
Matsalolin Sallah: Haqiqa matsaloli ko kurakurai da ake aikatawa a sallah wasu abubuwa ne da ba zai yiyu mu yi bayaninsu duka a nan ba, sai dai mu ďauki waďanda Allah Ya ba mu iko.
Daga cikin kurakurai na sallah akwai:
Rashin ilimi: Haqiqa rashin ilimin yadda za mu bauta wa Ubangiji wata matsala ce mai girman gaske, kasancewar shi Musulunci addini ne da be bar mu cikin duhu ba, don haka ya zama wajibi mu ďau littafi mu je wajen malamai don koyon yadda ake sallah, domin yanzu abin zai ba ka mamaki yadda za ka ga matasanmu wasu suna yin sallah ne dai kawai amma abin ya fi kama da exercise, don ba su iya sallar ba kuma girman kai ya hana su su je su koya, wannan matsalace mai girman gaske.
Qin yin sallah yadda Annabi (ﷺ) ya koyar: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ku yi sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah.” Wannan ke nuna cewa wajibi ne mu nemi sanin yadda Annabi ya kasance yana yin sallah, domin duk wanda ya yi sallah sa6anin yadda Annabi ya yi, to fa sallarsa ba ta inganta ba, kamar yadda wannan hadisin ya nuna kuma malamai suka yi bayani.
Rashin Ikhlāsi: Rashin tsarkake niyya a cikin sallah na iya gur6ata sallar mutum, don haka wajibi ne mu tsarkake niyya a dukkan ayyukan ďa'a, kada mu yi don wani ya gani ya yaba, mu yi don neman yardar Allah (ﷻ).
Shagaltuwa da tunane-tunanen duniya: Rashin sanya kushu'i, wato natsuwa da halarto da girman Allah a cikin sallah kan iya rage ladar masallaci ko ya 6ata masa sallarsa, don haka abin da aka so shi ne masallaci ya jefar da duk wani tunanin duniya tun daga lokacin da ya fara sallah.
In shā Allah idan muka kiyaye waďannan abubuwa, to za mu gyara sallarmu. Zan dakata anan in shā Allah. Babu laifi a turo da gyara a inda na yi kuskure.
Allah Ya sa mu dace.
✍🏿Ayyub Musa Jebi.
(Ansar).
.
📚 Irshadul Ummah WhatsApp.
+2348166650256.