HUKUNCIN YIN QARYA DON NEMAN CIMMA WATA BUKATA :
TAMBAYA TA 2989
********************
Assalamu alaikum wa rahmatullah. Mallam na gama degree ne kuma shekaru na na service sun wuce da shekaru uku zan iya rage shekarun nayi service din. Allah ya saka da alkhairi.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah.
Godiya ta tabbata ga Allah, Salati da aminci su tabbata ga Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka da Sahabbansa da dukkan salihan bayin Allah.
Game da tambayar da ka turo tun acikin wata Sha'aban, sai yau Allah ya nufeni da ganinta, kuma ga amsarta kamar haka :
A'a bai halatta gareka ka Qara shekarunka arubuce ko ka ragesu bisa haqiqar yadda suke ba, domin yin hakan wani nau'i ne na Algus da kuma Qarya.
Kuma Manzon Allah ﷺ yace "WANDA YAYI MANA ALGUS TO BA YA CIKINMU". (Wato ba ya cikin mutane masu mutunci agun Allah).
Sahihu Muslim, hadisi na 101.
Hakanan kuma nau'i ne na Qarya. Gashi kuma Allah (SWT) ya gargadi bayinsa muminai game da muhimmancin yin gaskiya, a inda ya fa'da acikin littafinsa Alqur'ani cewa:
"YAKU WADANDA SUKA BADA GASKIYA!!! KUJI TSORON ALLAH KUMA KU KASANCE TARE DA MASU GASKIYA".
(Suratut Taubah ayah ta 119).
.
Kuma Manzon Allah ﷺ ya gargadi al'ummarsa cewa su guji yin Qarya. Yace "Ku kiyayi yin Qarya, domin ita Qarya tana jan mutum zuwa ga fajirci (bushewar zuciya, mugunta, da rashin imani) Shi kuwa fajirci yana jan mutum zuwa shiga wuta.
Mutum bazai gushe ba, yana yin Qarya kuma yana kokarin yin Qarya har sai an rubutashi agun Allah cewa shi makaryaci ne".
Sahihul Bukhary hadisi na 6094, da kuma Sahihu Muslim hadisi na 2607.
Kada ka damu da cewa ai mutane da yawa suna yin haka, Domin kuwa za'a yiwa kowa hisabi ne bisa gwargwadon abinda ya aikata. Kuma komai kankantar aikin sharri idan ka aikatashi sai ka ganshi acikin mizaninka. Kuma duk abinda gaskiyarka bata baka ba, Qarya ma bazata baka ba.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (09/06/2022 10/11/1443).