ZA MU IYA CIYAR DA KIFAYE DAGA MUSHE ?
Tambaya
Assalamu alaikum Malam, sau da yawa idan Kajin mu sun mutu mu kan jefawa kifi su cinyen mushen, shin ya halatta ??
Amsa
Wa alaikum assalam
A zahiri hakan ba daidai ba ne saboda an haramta cin mushe ne saboda manufofi Kamar haka:
1. Kasancewar ba a san cutar da ta kashe shi ba.
2. Dankarewa jini a cikin namanta, saboda ta mace kafin a yanka ta.
3. Allah ya bayyana cewa Mushe kazanta ne, kamar ya zo a suratul An'am.
Don neman Karin bayani duba: Makasidush Sharia indassa'ady shafi na: 302
Kasancewar jikin kifin Yana ginuwa ne da abincin da yake ci, cin sa zai iya zama hadari ga rayuwar bil-adama, wannan yasa ciyar da su da abinci Mai kyau shi ne ya dace da Sharia.
Duk Wanda ya kyautata sana'arsa, Allah zai sanya Masa albarka ya kuma habaka arzikinsa
Allah ne mafi sani
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
01/06/2021
Domin samun fatawoyin Malam Kai tsaye sai a kasance damu a
FACEBOOK⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
TELEGRAM⇨
https://t.me/Miftahulilm2
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248