ANA YI DA MATAR AURE!

ANA YI DA MATAR AURE! 


Dangane da yin Mutu’a da matar aure (watau matar wani) akwai ruwayoyi guda biyu masu ban mamaki waɗanda ya kamata mai karatu ya gan su da idanunsa. Ta farko an karɓo ta daga Falalu Maulan Muhammad binu Rashid, ya ce da Ja’afar Sadiƙ: “Ni na auri wata mace auren Mutu’a sai ya ɗarsu a raina cewa tana da miji.  Da na bincika sai na samu ashe tana da miji.  Sai Ja’afar ya ce: Don me ka bincika?!” *[Tahzibul Ahkam na Aldusi, muj. na 7 sha. na 253]*. A wata ruwayar, sai ya ce, “Wannan (binciken) ba ya kanka.  Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.” *[Furu’ul Kafi na Kulaini, muj. na 5 sha. na 469]*.  Ruwaya ta biyu ita ma Kulaini da kansa (watau Bukharin ƴan Shi’a) shi ne ya ruwaito ta. An karɓo daga Abanu binu Taglub ya ce: “Na ce da Abu Abdullahi (watau Ja’afar Sadiƙ) ni ina tafiya a kan hanya sai in ga mace kyakkyawa kuma ba ni da tabbas ko tana da miji ko karuwa ce. Sai ya ce:  Wannan (binciken) ba ya kanka.  Abinda yake kanka kawai shi ne ka gaskata ta dangane da kanta.” *[Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 462]*. (Watau idan ta ce ba ta da miji shi ke nan).  

Wannan yana nufin cewa shi ɗan Shi’a babu abinda ya dame shi! Idan al’amari ya motsa masa, to ko matar wa yana kamawa.   Shin muna iya cewa waɗanda suke zaune tare da Rafilawa suna cikin hatsari?  Amma ba wannan ne kawai hatsarin ba; ga wanda ya fi shi.  
 
*Ana Yi da Ƙaramar Yarinya!* 
Ana yin Mutu’a da ƙaramar yarinya wacce ta kai shekara goma. An tambayi Abu Abdullahi, “Ko mutum na iya yin Mutu’a da yarinya ƙarama? Sai ya ce: E, sai dai idan ƙarama ce ainun ta yadda ana iya yaudararta. Aka ce:  Nawa ne idan ta kai ba’a yaudarar ta?  Ya ce:  Shekara goma.” *[A duba Furu’ul Kafi, muj. na 5 sha. na 463; da Tahzibul Ahkam na Aldusi, muj. na 7 sha. na 255].*    
Imam Khumaini, shugaban ƴan Shi’ar duniya na wannan zamani, ya yi wani ɗan ijitihadi a nan. Ya ce ƙaramar yarinya da jaririya duka ana iya yin Mutu’a da su amma ba da haƙiƙanin saduwa ba, sai dai da sumbata da runguma da kuma abinda ya kira ‘cinyantaka’ [ *tafkhiz* ], watau mutum ya sa zakarinsa a tsakanin cinyoyinta.  Sai mai karatu ya gafarce mu saboda ruwaito wannan ɗanyar magana, maras daɗin ji, amma haka Imamin ya faɗi, kuma maganar tana cikin littafinsa da ya rubuta da hannunsa. *[A duba Tahrirul Wasila na Khumaini, muj. na 2 sha. na 241].*   

Wannan ijtihadi na Imam Khumaini ba a ilmance kawai ya tsaya ba; a’a ya aiwatar da shi a aikace.  Sayyid Hussaini Almusawi ya ba da labarin Mutu’a da Khumaini ya yi da wata yarinya mai shekara huɗu ko biyar a duniya, a lokacin da yake zaman gudun hijira a ƙasar Iraƙi kafin juyin juya halin da ya shugabanta a Iran, a shekara ta 1979. Mai son ganin wannan labari filla *–filla, sai ya duba Kashful Asrari na Almusawi, shafi na 35-37.*  Ba wani abu ya sa muka bi diddigin wannan mas’ala ba sai don mai karatu ya san cewa mutanen da gaske suke.  Allah ya yi mana *Alam Nasharaha!*


*- JERIN LITTAFAN SHI’A NA 4: "Auren Mutu’a a wajen Ƴan Shi’a" - na Prof. Umar Labɗo*

✍ *AnnasihaTv*

 ```- Ga masu son siyen littafan da ma wasu littafan Prof sai su tuntuɓe mu kamar haka``` ;

*Call/WhatsApp:* 08142286718

*Twitter:* https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
Post a Comment (0)