Asalin Maguzuwa Da Alaƙarsu Da Hausawa

Asalin Maguzuwa Da Alaƙarsu Da Hausawa



Mutane da dama sun daɗe su na da wata tambaya a zuciyarsu a kan su waye Maguzawa?

A wannan labarin za mu bayyana ko su waye Maguzawa, kamar yadda wani marubuci kuma manazarci Ibrahim Aminu Daniya, ya labarta wa kafar BBC Hausa.

Su dai Maguzawa mutane ne Hausawa da yawancinsu manoma ne kuma suke a ƙauyukan ƙasar Hausa.

Malam Ibrahim ya ce, mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙari, sai dai yawancinsu ba Addinin Musulunci suke bi ba, kamar waɗanda suke tare da su a yankunan da suke, amma daga baya sannu a hankali wasu daga cikinsu na shiga Musulunci.

Ya ƙara da cewa, al’adunsu da yarensu, da kuma sutura sun dace da na Hausawa musamman kafin Jihadin Shehu Ɗanfodio, kuma su na nan birjik a wurare da dama musamman kamar wasu ƙauyuka a ƙasar Kano da ma Katsina.

Abin da aka fi karkata a kai na tarihi a cewar masanin shi ne, mutane ne waɗanda suka zo daga Habasha tun ana kiransu ‘Majusu,’ suka riƙa sauya suna har aka dawo ana kiransu Maguzawa.

Da yawan masu tarihi na ganin cewa, su ne asalin Hausawa daga baya suka ilimantu suka zama Hausawan da aka sani a yanzu.

To amma ya ce, daga baya an samu ƙaulani, domin wasu na ganin cewa alama ta fi nuna cewa mutanen Afrika ta arewa ne, domin al’adar da ta fito daga nan irin tasu ce, kafin su dawo arewacin Afrika.

“Akwai mutanen da suka zo daga Habasha suka zauna a Dutsen Dala da ke Kano, kuma mashahurin sarkinsu shi ne Barbushe, waɗannan mutane sun riƙa bautar gumaka, su kuwa Maguzawa da aka sani a yanzu ba sa bautar gumaka, amma su na da nasu abubuwan na tsaface-tsaface.”

Har yanzu dai, ba a san Maguzawa da wani harshe ba in ba Hausa ba.

In Da Aka Fi Samun Su 

Masanin ya ce, an fi samun Maguzawa ne a ƙasar Hausa musamman ma a dazukan Kano da Katsina, akwai su su na nan amma sannu a hankali su na shiga cikin jama’a su na karɓar Musulunci, don haka, yanzu ƙalilan ne suka rage daga cikinsu.

Ya ce, wasu daga cikin al’adunsu da suka yi kama da na Hausawan da suka rungumi Musulunci a yanzu sun haɗa da na; Bukukuwan aure ko na mutuwa, da kaɗe-kaɗe da raye-raye.

“Sunayensu sun sha bambam da na Hausawan yanzu, domin su su na sanya sunaye ne daidai da yanayi ko lokaci.

Misali idan yanayin roron wake ne sai su ce ‘Ci Wake,’ ko idan lokacin damina ne sai su sa wa yaro suna ‘Damina,’ ko su sanya sunayen Aljanu saboda su ne abokan mu’amalarsu musamman wajen bori da sauransu.

Marubucin ya ci gaba da cewa, a yanzu dai babu wani ƙiyasi na yawan Maguzawan da suka rage a ƙasar Hausa, abin da kawai yake a fili shi ne, yawansu ya ragu, kuma ya na ci gaba da raguwa domin yawanci sun haɗe da sauran jama’a yadda in ba sun faɗa ba, ba za ka gane ba, don haka akwai yiwuwar watarana ma za su ƙare ɗungurungum.

Na ɗauko wannan rubutu ne daga shafin Taskar Nasaba da ke facebook. 
Post a Comment (0)