DUNIYAR MUTUWA // 02

DUNIYAR MUTUWA // 02


Bayan gama wayata da mataata, tunani ya tarun-min a raina, damuwata ta dinga qaruwa, na shiga zurfin tunani, ban Farka ba sai ji na yi Direba na Tambaya ta: Wai shin Yaranka nawa ne? Na ce: 4, 2 maza 2 mata. Ya ce: Allah ya shiryar maka da su! Na ce: Amin, kai ma haka.
Na kalli hanya, sannan na kalli sama ina kallon ta, na kalli rana, sai naga kadan ya rage ta faadi, na fadi ina mai qura kallo: Ya Allah, Rahmarka nake kwadayi yaa Rahmaan yaa Raheem! Ban Aune ba naji direba na neman izinina wai yana so ya kunna sigaari, sai na ce: Ya kai dan uwana, kai mutum ne me daraja, kuma ina tsammanin tattare da kai akwai Alkhairi mai girma, ya za ka yardarwa kanka ka qona kanka? Ka qona kudinka? Kuma ka tauye Addininka a dalilin Sigaari?
.
Kuma a qarshe ba ta amfaanarka sai dai cutar da kai? Sai ya ce: Yaa kai dan Halal, kamin Addu’a, wallahi nayi qoqarin barin shan ta cikin Ramadan da ya gabata amma na kasa. Sai na ce da shi: kai mutum ne da Allah ya ba shi iko amma ka kasa akan sigari? Na ci gaba da masa nasiha da shiryar da shi, shi kuwa yana saurare na, yana mai nadamar shan sigaari da yake yi, bayan kammalawata sai ya ce: In shaa Allah daga yau bazan sake shan sigaari ba! Na ce masa ina mai farin ciki: Allah ya Tabbatar damu akan Addini!
.
Kawai ni dai zan iya tuna cewa: na jingina kaina jikin qofar motar ina tunani, na rasa menene ya sa ni nake firgici, na rasa akan menene, ga shi inajin damuwa mai tsanani a wannan lokaci.
Kwatsam, Sai jin qara mai tsanani na yi, gaba daya ni da direba muka rikice, na san cewa Taaya ce ta fashe, sai na ce ya rage sauri, ka sanya alama (Signal) don sauran motoci su san mun samu matsala ne, shi kuwa ko magana baya iyawa, ya kankame sitiyaarin motar.

Alamun damuwa cike da Fuskarsa, lokaci qanqani motar ta hantsila bangaren daama (tabi Wrong way) ta dinga qundun baala, ni dai Allah ya taimake ni inata fadin “Laa ilaaha illallaah, Muhammadur-Rasulullaah” ina jin kamar ina daga muryata da ita ne, bayan nan na ji wani duwka mai qarfi ta qasan kaina, na ji tamkar harshen wutane saboda tsabagen zaafinta! Motar ta wuntsula ba adadi, har dai ta tsaya, a nan ne nayi yunqurin fitowa in miqe, amma na kaasa, na kaasa koda motsa ga6a 1 ta jikina, naji wani irin radadi wanda ban tabajinsa ba a rayuwata, na kaasa magana, idanuwana a bude suke, amma bana iya ganin komai in ban da duhu!

Zamu chigaba da yardar Allah....
Adam Sani Abu umayra 

Daga
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)