DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 27

▪️📚♦️ DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 27 ♦️📚▪️





✍️ Yusuf Lawal Yusuf

فَإِذَا بَلَغْنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمْسِكُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ أَوْ فَارِقُوهُنَّ بِمَعْرُوفٍ وَأَشْهِدُوا ذَوَيْ عَدْلٍ مِنْكُمْ وَأَقِيمُوا الشَّهَادَةَ لِلَّهِ ۚ ذَٰلِكُمْ يُوعَظُ بِهِ مَنْ كَانَ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ ۚ وَمَنْ يَتَّقِ اللَّهَ يَجْعَلْ لَهُ مَخْرَجًا (٢) وَيَرْزُقْهُ مِنْ حَيْثُ لَا يَحْتَسِبُ ۚ وَمَنْ يَتَوَكَّلْ عَلَى اللَّهِ فَهُوَ حَسْبُهُ ۚ إِنَّ اللَّهَ بَالِغُ أَمْرِهِ ۚ قَدْ جَعَلَ اللَّهُ لِكُلِّ شَيْءٍ قَدْرًا (٣) سورة الطلاق : ٢-٣

2. Idan kuma sun kusa isa ƙarshen iddarsu to ku riƙe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance yana ba da gaskiya da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita. 

3. Ya kuma azurta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al'amarinsa ne. Haƙiƙa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu. Suratuɗ Ɗalaƙ (2-3). 

*_Tafsiri:_*
A waɗannan ayoyi kuma Allah (Subhanahu Wata'ala) ya ci gaba da sanar da muminai hukunce-hukuncen saki da kome da jan hankalinsu a kan su kiyaye dokokinsa don su sami mafita a cikin al'amuransu. Allah (Subhanahu Wata'ala) ya bayyana musu cewa idan matan da suka yi wa saki na ɗaya ko na biyu suka kusa gama iddarsu, to auna da ɗayan zaɓi guda biyu:
1. Ko dai su yi musu komw idan suna son su riƙe su da kyautatawa da mutuntawa da kulawa da haƙƙoƙinsu. 
2. Ko kuma su rabu da su har su ƙare iddarsu ba tare da tsangwama ko matsanta musu ba, tare kuma da ba su cikakkun haƙƙoƙinsu ko ma kyautata musu da wani abin ihsani don rage musu zafin raɗaɗin rabuwa da kuma surutun mutane. 

Sannan Allah (Subhanahu Wata'ala) ya yi umarni idan maza za su yi kome ko za su rabu da matansu to su kafa shaidu biyu adalai a kan sakin ko komen, domin kauce wa duk wani saɓani ko rikici a gaba. Sannan ya umarci su ma masu bayar da shaida da su tsayar da shaidarsu a kan gaskiya tare da neman yardar Allah, watau kada su rage ko su ƙara a kan abin da suka sani.

Sai kuma Allah (Subhanahu Wata'ala) ya nuna wa muminai cewa, waɗannan hukunce-hukunce da dokoki da yake bayyana musu yana yin haka ne don su zamanto wa'azi ga wanda ya yi imanu da Allah da ranar alƙiyama, domin shi ne kawai wanda zai amfana da tunatarwa da wa'azi. Kuma Allah (Subhanahu Wata'ala) ya yi musu alƙawari da cewa, duk wanda ya tsare dokokinsa, ya yi aiki da umarninsa ya guje wa haninsa, to lalle zai sanya masa mafita daga duk wani ƙunci ko damuwa da zai faɗa cikinta, kuma zai azurta shi ta inda ba ya tsammani. Don haka mumini ya ci gaba da dogaro ga Allah da mayar da al'amuransa a gare shi, domin ya yi alƙawarin cewa duk wanda ya dogara gare shi cikin al'amuransa to shi ya ishe shi ga komai, kuma Allah shi ne mai zartar da al'amarinsa yadda ya ga dama babu mai hana shi ko wani abu ya gagare shi. Allah ya riga ya sanya wa komai iyaka da yake tuƙewa zuwa gare ta, don haka tsanani yana da iyaka, jin daɗi ma yana da iyaka babu wani abu mai dawwama har abada a nan duniya. 

*_Daga waɗannan ayoyi za nu mu fahimci abubuwa kamar haka:_*

1. Wajabcin kyautata wa mace a kowane hali, a lokacin rabuwa da ita ne ko lokacin ci gaba da zaman aure tare da ita. 
2. Muhimmancin kafa shaidu biyu adalai lokacin saki da lokacin kome, don guje wa rigingimu, kamar ta yi da'awar ita matarsa ce bayan ya muti, ko ƴaƴansa su yi iƙirarin cewa ubansu ya riga ya sake ta tun kafin ya mutu don haka ba ta xa gadonsa, ko ta musunta cewa mijinta ya dawo da ita don tana son ƙare iddarta ta auri wani ba shi ba, ko kuma don kore zargi da surutun mutane. 
3. An kwaɗaitar da mutane da su riƙa tsayar da shaida don Allah, domin zai iya zamantowa akwai wahala gare su su bar al'amuransu don zuwa bayar da shaida, ko kuma domin nisan wurin bayar da shaidar, ko wani dalili da zai sha musu kai, sai Musulunci ya kwaɗaitar da su cewa su yi komai don Allah saboda su samu yardarsa da lada a wurinsa. 
4. Babu wanda yake amfana da wa'azi da tunatarwa kamar mutumin da ya yi imani da Allah da ranar lahira. 
5. Duk wanda ya kiyaye dokokin Allah (Subhanahu Wata'ala) ya yi aiki don neman yardarsa, to lalle Allah zai yi masa kyakkyawar sakayya a duniya da lahira. Daga cikin sakamakon da zai yi masa shi ne ya samar masa mafita daga duk wani runtsi da damuwa. Wanda kuwa ya ƙi bin dokokin Allah to dole ya yi ta gamuwa da matsaloli iri-iri a rayuwarsa ta duniya sannan ya gamu da mummunan sakamako a lahira in ya mutuybai tuba ba. 
6. Taƙawa watau kiyaye dokokin Allah tana daga cikin hanyoyin samun arziki daga Allah. 
7. Dogaro ga Allah jari ne babba ga bawa wanda babu abin da ya kai shi. 
8. Wajibi ne mumini ya ba da gaskiya da cewa komai a wurin Allah yana da lokacinsa da iyakarsa, don haka kada ya bari baƙin ciki ya kashe shi don ya rasa wani abu da yake so, komai yana da lokacinsa a wurin Allah. 

Tsakure Daga Cikin Fayyataccen Bayani Na Ma'anoni Da Shiriyar Alƙur'ani, Tafsirin Sheikh Dr. Muh'd Sani Umar Rijiyar Lemu.

*_Telegram:_* https://t.me/DDAMG

*_21st Rajab, 1442A.H (05/03/2021)._*
Post a Comment (0)