HUKUNCIN YIN SAKI UKU A CIKIN FUSHI
https://chat.whatsapp.com/DWYcMPuRQsVETkdAMC4evr
:
*TAMBAYA*❓
:
Asslaam Alaikum Wa Rahmatul Laah.
Mijina ya sake ni a cikin fushi kuma daga baya ya yi nadamar yin hakan, har ya nemi in koma amma na ƙi, har sai na yi wani auren. Daga baya muka yi auren sirri da wani, wanda bayan saduwa guda ya sake ni ya gudu. Iyayena kuma suka ce ba su yarda da wannan auren ba! Ni kuma ina son komawa gidan mijina wurin ’ya’yana mata guda biyar. Don Allah wanne taimako za ku yi a kan wannan?
:
*AMSA*👇
:
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
1. Taimakon da kowanne musulmi zai iya yi miki a nan sai dai ya bayyana miki hukuncin ALLAH Subhaanahu Wa Ta’aala kawai a kan al’amarin idan ya sani. Sannan kuma ya umurce ki da yin haƙuri wurin yin biyayya ga dokokinsa, a matsayinki na musulma wacce ta yi imani da shi, kuma take da aƙidar sallamawa da miƙa wuya gare shi a cikin komai.
2. Malamai sun kasa sakin aure nau’i-nau’i ne: Akwai Sakin Sunnah akwai kuma Sakin Bidi’a. Saki uku yana iya shiga kowanne daga cikin nau’ukan guda biyu.
Idan Saki-uku yana nufin saki na-uku ne, watau ya sake ta saki na-uku a bayan wasu saki ɗai-ɗai har guda biyu da suka gabata, wannan ya shiga nau’in saki na Sunnah ne. Shi ne kuma wanda Nassin Alqur’ani ya tabbatar da hukuncinsa cewa:
فَإِن طَلَّقَهَا فَلَا تَحِلُّ لَهُۥ مِنۢ بَعۡدُ حَتَّىٰ تَنكِحَ زَوۡجًا غَیۡرَهُۥۗ
Ba za ta halatta gare shi ba a bayan haka, har sai ta auri wani mijin da ba shi ba.
(Surah Al-Baqarah: 230)
Idan kuma Saki Uku yana nufin saki sau uku ne a lafazi guda, kamar ya ce: ‘Ya sake ta saki uku’, ko kuma a mazauni guda, watau kamar ya ce: ‘Ya sake ta! Ya sake ta! Ya sake ta!’ A nan malamai tun daga zamanin Sahabbai har zuwa yau sun yarda cewa shi sakin bidi’a ne. Inda suka yi saɓani dai shi ne: Ko za a ɗauke shi a matsayin ukun ne, ko kuwa dai a matsayin ɗaya ne? Maganar da ta fi inganci da ƙarfi ta fuskar dalilai kamar yadda manyan malamai muhaƙƙiƙai suka tabbatar ita ce ta ƙarshen. Watau shi saki ɗaya ne wanda kuma mijin yake iya yin kome a cikinsa, kafin ta gama idda.
Wannan maganar a wurin fatawa kenan, amma a wurin hukunci dole ma’aurata su koma ga irin hukuncin da Alƙalin Musuluncin yankinsu ko garinsu ya ɗauka daga cikin ra’ayoyin guda biyu, don gudun kar a janyo hayaniya a tsakanin al’umma. Wal-Laahu A’lam.
3. Amma shi Auren sirri, watau Auren Ɓoye: Shi ne auren da namiji da mace suke ƙullawa su kaɗai a saƙo, ba tare da sanin waliyyin matar, ko kuma shaidu ba. Duk malamai sun haɗu a kan cewa: Wannan auren ɓatacce ne, ya fi kama da auren daduro wanda Alƙur’ani ya hana:
فَٱنكِحُوهُنَّ بِإِذۡنِ أَهۡلِهِنَّ وَءَاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِ مُحۡصَنَـٰتٍ غَیۡرَ مُسَـٰفِحَـٰتࣲ وَلَا مُتَّخِذَ ٰتِ أَخۡدَانࣲۚ
Ku aure su da izinin waliyyansu, kuma ku ba su sadaƙoƙinsu yadda ya dace da shari’a, suna masu kamun kai ba mazinata ba, ba kuma masu yin daduro ba.
Surah An-Nisaa’i: 25.
Haka kuma Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
أَيُّمَا امْرَأَةٍ نَكَحَتْ بِغَيْرِ إِذْنِ وَلِيِّهَا، فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ! فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ!! فَنِكَاحُهَا بَاطِلٌ!!!
Duk matar da ta yi aure ba tare da izinin waliyyinta ba, to aurenta ɓatacce ne! Aurenta ɓatacce ne!! Aurenta ɓatacce ne!!!
Ahmad da Abu-Daawud da At-Tirmiziy da Ibn Maajah suka riwaito, Shaikh Albaaniy ya ce: Sahihi ne a cikin Al-Irwaa’: 1840.
4. Daga waɗannan nassoshin ya bayyana a fili cewa:
Idan sakin da mijin ya yi miki saki uku ne a cikin kalma guda ko a wuri guda, sannan kuma ya nemi ki dawo ku Cigaba da zama bayan ya yi nadama a kan hakan, wannan ba laifi ba ne, a maganar da malamai muhaƙiƙai suka rinjayar, kamar yadda ya gabata. In da kin amince da shi a kan haka tun a lokacin to da wataƙila a yanzu an wuce wurin, da sai dai ki riƙa bayar da labarinsa kawai.
Dogewan da kika yi cewa dole sai kin sake yin aure da wani namijin da ba shi ba, wannan shi ya kai ga faɗawa a cikin kuskure ba-biyu: Watau Auren Sirri, wanda kuma kamar yadda muka ji daga harshen Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): Shi ɓataccen aure ne. Don haka ne ma iyayenki suka ƙi amincewa da shi.
Shi ma wanda kuka yi da shi ya gudu, don yana tsoron kar asirinsa ya tonu, kamar yadda kika bayyana a farkon fatawarki.
4. Don haka, hanyar da ta rage muku ke da tsohon mijinki ita ce: Ku yi haƙuri har sai kin je kin sake yin wani aure sahihi da sanin iyaye da sadaki da shaidu da komai, kuma auren ya zama na soyayya ba na haɗin baki ba da wani mijin da ba wancan ba. Kuma idan daga baya ya sake ki a bayan sahihiyar saduwa, to a nan ne kike iya komawa ga mijinki na farko.
Dalili: Saboda hadisin da Al-Imaam An-Nasaa’iy da Ahmad suka riwaito daga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) cewa: An tambayi Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) game da mutumin da ya saki matarsa, kuma ta je ta auri wani mijin da ba shi ba, ya tare da ita, amma sai ya sake ta tun bai sadu da ita ba, shin ko tana halatta ga mijinta na farko? Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
لاَ حَتَّى يَذُوقَ الآخَرُ عُسَيْلَتَهَا وَتَذُوقَ عُسَيْلَتَهُ
A’a! Har sai ɗayan ya ɗanɗana zumanta, ita ma ta ɗanɗana zumansa!
(Sahih An-Nasaa’iy: 3407)
Wal Laahu A’lam.
Amsawa: Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana