JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 17
ISA AS
Koda yake tarihi ya rawaito yaran da suka yi magana tun suna jarirai kafin Isa AS sai dai zamanin ba irin na yanzu ne da duniya ta dawo tafin hannun mutane ba, su dai banu Isra'ila sun fara ganin abubuwan ta'ajjubi a gidan Imrana, yadda Maryam ta riqa zama cikin abinci kala-kala wadanda ba masu sauqin kudi ne ko samu ba, da yawa an sakankance cewa daga Allah SW ne suke zuwa, samunta da yaro bayan an san gidan da ta taso da irin tarbiyyar da ta samu sannan babban abu ba wanda ya taba ganinta da wani, ba a taba ganin alamar ciki tare da ita ba sai ga yaro wannan kawai ya isa a gasgata ta.
.
Sai dai kuma tana tare da banu Isra'ila ne, sannan a zamani mai matuqar rudani wanda ba mai shiryarwa, in an same shi ma kashe shi ake yi, ba a buqatar wani wa'azi sharholiya kawai ake yi ta dibar albarka, to ko manzon ne ya zo musu qaryata shi za su yi bare kuma wata waliyiyar Allah mai bauta, shi ya sa da aka yi mata busharar samun da da abinda zai zama hankalinta ya tashi ta ce { رب أنى يكون لي ولدٌ ولم يمسسني بشر قال كذلك الله يخلق ما يشاء إذا قضى أمراً فإنما يقول له كن فيكون} Ubangiji, ta ya zan sami da gani ba wani mutumin da ya taba tabata? Ya ce: Haka Allah yake halittar abinda ya ga dama idan ya so yanke wani al'amari sai ya ce "Zamo" sai ya zama) Ali Imran47.
.
A dalilin dabi'arsu da halayansu Allah SW ya fitar da Maryam ita kadai bayan mahaifiyarta ta girma ta wuce haihuwa, wannan wata karama ce, ta girma a hannun annanin Allah, wurin bauta ne gidanta, ga wasu karamomi dake nuna kusantakarta da Allah SW amma bai sa banu Isra'ila su sunkuya wa yardar Allah ba sai da suka tambaye ta inda ta samo yaro, wannan daidai ne, amma in aka gaya musu kuma aka ba su gamsasshiyar hujja ya kamata su yarda su miqa wuya, amma ina! Suna da abinda yake cikin zuciyarsu.
.
Babban abinda zai gamsar da su dangane da samun jaririn shi ne a sami shedar amintaccen mutumin da aka yi lamarin a gabansa, sai Allah SW ya sa jaririn ya zama sheda, wannan kam kat ne, hujja ce da ba wanda ya isa ya qaryata ta, jaririn da aka haifa din ne shedanta, ga kuma wata mu'ujiza wace ba wanda ya taba ganin irinta, jariri na magana, ba ma magana kadai ya yi ba har da tabbatar da abinda ya faru na samuwarsa, shi ne a yau aka rabu zuwa gida 4;
1) Akwai masu bautar Maryam AS saboda abinda ya faru, tsarkinta na dabi'a da kuma iya kawo yaro kamar Isa AS ba tare da miji ba.
.
2) Masu bautar Isa AS, saboda kasancewarsa ruhi daga Allah, ya zo ba uba, don haka shi ma Allan ne a bayan qasa.
3) Masu cewa shi dan Allah ne ko dayan sassa uku na kasantuwar Allan.
4) Masu ajiye shi a matsayin manzon Allah kuma bawansa, musulmi ma haka suka dauke shi, sun ajiye shi ne a matsayin bawan Allah kuma manzonsa,
Allah SW na sane da cewa wasu za su bauta masa, koda yake sun sami sabani wajen fahimtar waye Allan, mahaifiyarsa ko shi ko hadin uku a qarshe dai Isa AS abin bauta ne gare su.
.
A lokacin da banu isra'ila suka tare Maryam AS don su yi mata tambayar qwaqwab, suka ce mata babanta mutumin kirki ne mahaifiyarta ba karuwa ba ce, ta san abinda suke nufi don ita ma abin ya dake ta, duk da haka sai ta nuna shi don su tambaye shi, nan take Isa AS ya fara da cewa: { إني عبد الله آتاني الكتاب وجعلني نبياً} (Ni bawan Allah ne da ya ba ni littafi ya kuma sanya ni annabi) Maryam30, ikon Allah kalmarsa ta farko a bayan qasa ita ce shi bawan Allah ne, kafin ya tabbarar da manzancinsa da Allah SW zai aiko shi da shi nan gaba.
.
Lokacin da banu Isra'ila suka juya baya suka kafurce, suka fada cikin lamuran sha'awoyi, ga zalinci da barna kala daban-daban a bayan qasa, suka qaryata hisabi sai Allah SW ya turo musu Isa AS, ya sanar da shi Attaura da Injila, ya miqe da koyar da su amma suka kau da kai kamar ba da su yake ba, har sai da ya ce: Wai su wa za su taimaka min ne zuwa ga Allah? Nan ne aka sami 'yan wasu qalilan da suka ce mu ne mataimakanka, wasu kuma suka kafurce masa suka qi yin imani da shi.
.
Lokacin da suka lura da cewa ya fara samun mutane a tsakankanin talakawa da mabuqata sai suka qulla masa wani sharri, suka aika wa sarkin Rum cewa ga shi yana hada wata zuga wace za ta qarar da mulkinsa nan gaba, shi ne shi kuma ya lashi takobin batar da shi, ya yi umurnin a kama shi a tsire shi kowa ya huta, annabi Isa AS yana fuskantar kaifi biyu ne tun a lokacinsa, akwai wadanda ba su yi imani da shi ba kwata-kwata kuma qoqari suke yi su ga bayansa, da kuma wadanda suka yi imani da shi yana qoqarin ba su kariya da shiryar da su hanya madaidaiciya.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248