JAGORANCIN MUSLUNCI DAGA JIYA ZUWA YAU // 18
MUHAMMAD SAW
A muslunce shi ne annabin qarshe kuma ba wani annabi bayansa, koda yake tun farko akwai banu Isra'ila a yankin Larabawa kafin turo shi a matsayin manzo, sai dai shi a Makka aka haife shi nesa da inda suka tare suna jiran tsammani, sun ji a wurin masu addininsu cewa akwai wani annabi da zai zo kuma shi ne annabin qarshe, sun riqe lissafinsa da wurin da zai fito, kuma sun zo wurin sun zauna da burin ya fito a cikinsu, ashe sun zauna a inda zai rayu ne ba mahaifarsa ba.
.
Banu Isra'ila ba su san komai game da haihuwar ma'aiki ba sai bayan ya girma kuma an turo shi da saqo, masamman dai dawowarsa Yasrib wato Madina din in da zai rayu tare da su, tarihi ya nuna mutanen kirki sun riqa ba da shawarar cewa a dena yawo da shi tsoron gamuwarsa da Yahudawa, ya rayu ne cikin Larabawa zalla, fitowarsa a cikinsu kuwa mu'ujiza ce ta masamman, domin al'ummar Annabi SAW mutane ne masu ilimin Kimiyya da fasahar qere-qere, wadanda bayan doron qasa sai da suka kai bincikensu sararin samaniya da qaqashin teku zuwa cikin duwarwatsu.
.
Duk annabin da zai zo musu to fa mu'ujizarsa za ta hada da tsabagen ilimi, sai Allah SW ya fitar da shi a cikin al'ummar da ba rubutu ko karatu, haka ya fito ba a san wani malaminsa ba, shi ma ba rubutun ba karatun, yadda mu'ujizar za ta fito kenan sosai, domin kuwa duk ilimin duniya da ake togo da shi yanzu Annabi SAW ya zo da shi, ba wani fanni na Kimiyya da Fasaha wanda Annabi SAW bai shinfida masa tsabagen ilimi ba, wannan ya sa in Nasaran suka qare bincikensu daga baya suka sami cewa Annabi SAW ya yi bayaninsa sama da shekara dubu da suka gabata sai ka ga sun muslunta.
.
Don sun san cewa wannan ya wuce qwaqwalwar dan-adam wani abu ne daga Allah SW, yanzu akwai kayan gwaje-gwaje sannan mutum tun yana yaro yake karatun kimiyyannan amma sai ya taras wani ya riga ya yi qarin haske akai tun dauri lokacin da ba ilimin a wurin kowa, yankin kuma na wadanda ba rubutu ne ba karatun, ba wata na'ura da za ta iya taimakawa wurin bincike, wannan kam wani lamari ne da bai kamata a musanta saqon Annabi SAW ba, masamman al'ummar wannan lokacin da suke togo da ilimin.
.
Annabi SAW ya yi maganar teku da abubuwan dake cikinsa da ma rabe-rabensa da kalolinsa da inda suke haduwa su qi cakuduwa, ya yi magana kan dabbobi da wadanda ke da hatsari ga rayuwan dan adam kamar dai alade da kare, sai kuma sararin samaniya da halittun rana, wata da taurari har da magudanansu da masaukansu, ya yi maganar haskensu yanda daya ke karba daga wani, da taurari da alaqarsu da rana da ma yadda suke, daganan sai yadda ake hada iskokin da za su samar da ruwan sama, ba wannan iskar da muke shaqa ba ce, yanzu an fassara su da "Oxygen" da "Hydrogen".
.
Annabi SAW ya fado tsarin ginin gira-gizai a sararin samaniya, bayan lokacin ko jirgin sama babu bare 'yan sama jannati, ba nan kadai ba ya yi tabo halittar qasa da rabe-rabenta, kai hatta mu 'yan adam daga inda ruwan maniyyin ke fara gangarowa na mace da na namiji, da haduwar qwanyi, samun ciki, hatta adadin kwanakin da dan ke juyawa daga wani rukuni zuwa wani ya fadi, ga wasu abubuwan da ya riqa fadin za su faru kuma ana ta ganinsu yanzu, kenan Nasarannan su ya kamata su fara yin imani da Annabi SAW a yauzu, domin duk abinda suke tunqaho da shi Annabi SAW ya fado shi da shekara dubu da doriya da suka gabata.
.
Don Larabawa dama ba su yi adawa da ma'aiki SAW ba, don ba su dauke shi matsala a cikinsu ba, sun yarda da shi sun karbe shi hannu bibbiyu, suna ma kiransa amintacce, in ya yi hukunci sun karba tare da qarancin shekarunsa, matsalarsa da su ta faro ne yayin da ya fara sukar allolinsu, zuwa lokacin da ya ce su guje su su dawo bautar mahalicci, a zatonsu addinin da suke yi shi ne daidai, Shedan kuma ya sami damar qara nisanta su, sabanin banu Isra'ila wadanda addinin ne kwata-kwata ba sa so, sharholiyarsu suke son yi ba tare da an takura su ba.
.
Za mu ga cewa muslunci ya fara dawowa tare da samun matsuguni a inda dankin Allah mafi girma yake wato Makka, sai dai mabiya wasu addinan sun yi tsayuwar daka wurin tunkude shi, da haka aka ba Annabi SAW damar hijira, lokacin farko kenan da addini ya fara fita wuri mai nisa wato Habasha, zuwa tarewarsa kacokan a Madina, inda Yahudawan suke tsammanin samunsa, da ganin Annabi SAW sun san manzo ne sai dabi'arsu ba boyayyiya ba ce tun-fil-azal.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248